Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa shawarar sulhu da ‘yan bindiga ta fito ne daga al’ummar jihar, waɗanda suka roƙi a kawo ƙarshen tashin hankalin da ya jima yana laƙume rayuka da dukiyoyi. Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda halin da jihar ke ciki ba zai bar shi da wani zaɓi ba face ya bi shawarar jama’a.
Da yake magana a wani shirin BBC Hausa, Gwamna Sani ya kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na tattaunawa da ‘yan bindiga, inda ya ce burinsa shi ne daƙile hare-haren da suka addabi wasu sassan jihar. Ya ƙara da cewa Sarkin Birnin Gwari tare da wasu daga cikin al’ummar yankin sun kai masa ziyara, inda suka roƙi a tattauna domin kawo ƙarshen asarar rayuka, da ƙone gidaje, da lalata gonaki.
Gwamnan ya bayyana cewa ya gana da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, kafin yanke shawarar fara sulhu da ‘yan bindiga. Ya ce, “Na yanke shawarar sulhu ne don kada na rasa ko da mutum guda daga cikin jama’ar jihar Kaduna. Idan ba haka ba, zan fuskanci tambaya a ranar ƙiyama, ganin cewa na ɗauki alƙawari kuma na yi rantsuwa da Alkur’ani.”
Sani ya ce matakin ya fara samun nasara, inda ‘yan bindigar suka sako mutum 200 da aka sace a ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari. Ya nuna ƙwarin guiwa cewa yarjejeniyar za ta kawo zaman lafiya, ta yadda manoma za su koma gonakinsu, kuma kasuwanci zai bunƙasa.
Jihar Kaduna dai ta daɗe tana fama da hare-haren ‘yan bindiga, musamman a ƙananan hukumomin Chikun, Kagarko, Giwa, Kajuru, da Birnin Gwari, tare da kai hare-hare a manyan hanyoyin jihar. Gwamnan ya kuma tabbatar wa jama’a cewa ba a biya ko da naira ɗaya ba domin cimma wannan sulhu, tare da yin aiki da jagorancin masu addini da sarakunan gargajiya, wanda ya ɗauki watanni shida kafin sanar da jama’a.
