Ko a tarbiyya za a gane ‘ya’yan mace mai ilmi – Dakta Erisa Danladi

Spread the love

“Ina cikin mata masu ƙananan shekaru da suka yi fice a duniya”

 Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe

Dakta Erisa Sarki Danladi, Babbar manomiya ce kuma yar gwagwarmaya a ɓangaren ayyukan raya karkara, kuma mai fafutuka tsakanin ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba wato NGO’s. Mace mai ƙoƙarin taimakon marasa galihu. Gatan marar gata. Ita ce babbar daraktar ƙungiyar nan mai suna ‘Motherhen Deɓelopment Foundation’, da ta ke koyawa mata da matasa sana’o’in hannu, sannan kuma ko-odinata ce ta Arewa maso Gabas ta wata ƙungiyar tallafa wa mata ‘yan siyasa wato ‘women in political empowerment’, da sauran ƙungiyoyi da dama masu zaman kansu.

A tattaunawarta da shafin Gimbiya ta jaridar Manhaja, ta bayyana tarihin rayuwarta da kuma irin gwagwarmayar da ta ke yi a rayuwa:

MANHAJA: Mene ne tarihin rayuwarki?

DAKTA ERISA: Ni sunana Danladi Erisa Sarki. Ni ‘yar garin Dala Waja ce, ‘yar ƙabilar Waja a ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe. Kuma ina daga cikin mata masu ƙananan shekaru da suka yi fice a duniya, ba ma a Nijeriya kaɗai ba, daga wannan yanki namu na Gombe ta Kudu har wajen ƙasar nan.

An haife ni a shekarar 1981, na yi firamare ta ‘Ya’yan Ma’aikatan FCE (FCE Staff School) daga nan sai na tafi kwalejin ‘yan mata ta Gwamnatin Tarayya FGGC da ke garin Owere a Jihar Imo, lokacin rikicin mulkin June 12, ban gama a can ba na dawo Gombe inda na kammala sakandare ɗina a Gombe High School a shekarar 1999. 

Da na gama sai na yi JAMB na tafi Jami’ar Maiduguri da ƙudurin karanta fannin shari’a wato ‘law’, sai zafin garin Maiduguri ya hana ni zama, sai na dawo Yola na rubuta IJMB na tafi Jami’ar Jos na sake cika law. Ba su ba ni ba, suka ba ni ‘Theater and Communication’, haka na haƙura na karɓa har na yi digiri ɗina na farko. Ina digiri ɗin ina kuma yin difloma a ‘law’, duk dai saboda wai in karanta ‘law’, na zama lauya, amma Allah bai nufa ba. 

Da na gama digiri sai na tafi hidimar ƙasa NYSC a Inugu, bayan na gama, sai na cika neman aiki a bankin zenith. Suka kira ni jarrabawar ɗaukar aiki wato ‘Interɓiew’, shiru ba su kira ba, ina nan ina jira shiru. Sai na fara zuwa walka aikin gona na kuɗi, don na fitar da tsammani.

Ina nan har na fara ta wa noman. Da taimakon Allah sai wata shekara kawai sai gani na noma buhun masara 78. Hakan ya sa na ji ba na sha’awar aikin gwamnati. Ina noma, ina bincike wato ‘research’ akan al’amuran yau da kullum, kuma noman damina kawai na ke yi ban da na rani. 

Da haka na sake koma wa Jami’ar Jos a sashin ‘Theater and Communication’ na yi digiri na biyu. Daga nan na sake komawa yin Phd wato digiri na uku a ‘Theater and Community deɓelopment’ saboda na ƙware wajen aikin al’umma a karkara, inda na ke mayar da hankali akan ɓangaren cigaban jinsi da mata.

Kin fuskanci ƙalubale a rayuwarki?

Gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai domin kafin na yi ƙarfi mijina ya rasu, ya bar ni da yara ina ta faɗi-tashin rayuwa. Ba na aiki sai noma kuma an fi sanin maza da noma, ba mata ba. Babu mai taimaka min. Da haka na kai inda na ke yanzu. 

A irin aikin al’umma da na ke yi ne ya ɗaga ni, domin na zaga duk garuruwan Nijeriya saboda wannan aikin na al’umma ‘Community Work’.

Na san ba za a rasa nasarori ba?

Nasara kan ba za ta misaltu ba, domin aikace-aikacen da na ke yi ya ɗaga ni a idon duniya. Na samu ɗaukaka sosai yadda ba ka tsammani, domin na san manyan mutane kuma na ziyarci ƙasashe masu yawa a duniya.    

Mene ne burinki a rayuwa?

Burina shi ne in taimaka wa wanda bai da yadda zai yi a rayuwa ko wanda bai da hanyar dogaro da kai. Idan na taimaka mu su a lokacin ina ƙara samun nitsuwa a raina da kuma yin bacci mai daɗi, saboda na gyara kusancina da ubangiji.

Me ya ba ki shawa’ar son yin siyasa ?

Abinda ya sa ni sha’awar siyasa shi ne; saboda ni ‘yar ƙauye ce kuma garinmu ba hanya. Ina son ganin na taimaka wa ƙauyenmu, shi ya sa a kullum ba ni da buƙatar da ta wuce ta zama kansila ko shugabar ƙaramar hukuma, kusa da al’ummata dan na samu kusanci da gwamnati ta yadda zan ga garinmu ya shiga sahun garuruwan da suka cigaba, suke da hanya da ruwan sha da wutar lantarki da kuma asibiti na zamani.

Ta ya kika haɗu da mijinki?

A lokacin ina jami’a mu ka haɗu da shi. Ina aji biyu, shi kuma yana ajin ƙarshe na gamawa. A nan mu ka haɗu har Allah ya yi mu ka yi aure. Amma yanzu Allah ya yi masa rasuwa.

Waɗanne irin tufafi kika fi so?

Na fi sanya doguwar riga ta atamfa, sannan na sanya gyale. Don ko ƙasashen wajen da na ke zuwa riga da gyale za ka ganni da shi ba wani kaya daban ba.

Ko za mu iya sanin ƙungiyoyin da kike ciki? 

Ni mamba ce a ƙungiyar Mata ‘Yan agajin Coci wato ‘Girls Bridge’ tun ina ƙarama har na girma ina ‘Red Cross’ da Sonta (Society of theater Arts) ƙungiyarmu ce ta makaranta. Sannan ina mamba a NIM ‘Nigeria Institutes of Management’. Na yi aiki da wata ƙungiya mai suna ‘Published what you pay’, ƙungiya ce da ta ke kula da yadda ake haƙo man fetur a Nijeriya. Ni ce wakiliyarsu ta ƙasashen Yammacin Afirka. Na yi aiki da BBC ‘Media Action’ da kuma ‘Bills da Melinda gate’.

ƙasashen nawa kika ziyarta?

Suna da yawa. Na je Ghana; Dakar, Senegal, Guinea Conakry, Liberia, Egypt, Dubai, Turkey, New York, westham, Belgium, South Africa, Georgia, Benin, Togo, Gambia, sannan na je Iɓory Cost da Nijer da Mauritania, Zimbabwe, Mali, Burkina Faso da Cape ɓade da sauransu.

Kin taɓa cin wata kyauta ko aka karramaki?

Na samu kyaututtuka daban daban, domin tun ina jami’a na fara samun kyauta ta wacce ta fi kowa yawan murmushi (Best smiles) saboda gaskiya ni ban iya tsumewa ba, na kuma samu kyauta daga kwamandanmu a lokacin muna hidimar ƙasa NYSC. ƙaramar Hukumar Inugu su ma sun ba ni kyauta ta ‘yar hidimar ƙasar da ta fi ƙwazo. Ma’aikatar Matasa ta ƙasa su ma sun ba ni lambar yabo mai suna ‘top 12’. Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya Dame Patience Jonathan ta sa an bani lambar yabo a ‘Yeshu’a international school of theology’ a United Kingdom digirin girmamawa ne a shekara ta 2013 tun ban gama digirina na biyu ba.  

Ko akwai wasu kwasa-kwasai na musamman da kika yi kafin ko bayan kammala digiri?

Na yi kwas da ‘Peer Education Training’ BCC ‘Behaɓioral Communication Change’, da kuma OɓC ‘Orphan and ɓulnerable’, na je kwas na ‘Nigerian Institute of Management’, na kuma yi kwas na ‘Desplay Africa’, ‘Democracy series participation learning and achieɓed youth’, na je ‘eɗchange programe’ a Ghana, na yi kwas kan horar da mata ‘yan siyasa ‘women political empowerment’, na yi kwas na ‘gender and transformatiɓe leadership’. 

Me ya fi burge ki?

Ina son mai taimako, domin ko ni ce na taimaki wani ina jin na burge kaina saboda taimako yana da kyau a rayuwa, kuma ko ban san ka ba idan da hali idan na taimaka ma ka ina jin daɗi.

Yawan iyali

Ina da yara bakwai da kuma ‘yan’uwa waɗanda su ma iyalai na ne.

 Wacce shawara za ki ba wa iyaye?

Ina mai bai wa iyaye shawara su dinga barin ‘ya’yansu mata suna samun ilimin zamani, domin ilimi yana da muhimmanci gare su, saboda ni ma duk waɗannan nasarori da na samu da ba don albarkacin karatu ba da ba zan same su ba.

Shi ilimi musamman ga ‘ya mace yana da kyau, domin ko wajen tarbiyyar yara za a gane ‘ya’yan mace mai ilimi da na marar ilimi. Ban ce kar a bar namiji ya yi karatu ba, amma dai a kula da na ‘ya mace sosai, kamar iyaye da suke ƙin bai wa ‘ya’ya mata ilimin suna ɗora masu talla, su sani fa wajen talla kasuwanni ne da tashoshi kuma waje ne mai hatsarin gaske da zai yi saurin lalata tarbiyyar yara, domin irin kalolin mutanen da suke mu’amalla a wajen.    

Mun gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi