’Yan APC shiyyar Arewa Maso Yamma sun karrama Gwamna Badaru

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC na arewacin Nijeriya sun karrama Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar saboda ƙoƙarinsa na cusa wa matasa ɗa’ar siyasa.

An yibikin karramawar ne a ranar Asabar da ta gabata a filin Foke na Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhd Sunusi da misalin ƙarfe goma na dare.

Bikin ya samu wakilcin matasa daga jihohin Zamfara, Kebbi, Kaduna, Katsina, Sakkwato, Kano da jihar Jigawa mai masaukin baƙi.

Matasan sun shirya gagarimar liyafa ga Gwamna Badaru, har ma an yi yayyafin Naira ga matasan mawaƙa da suka baje basirarsu a wurin taron liyafar, suka koɗa Gwamna Badaru a wajen bikin karramawar.

Shi ma danyake jawabi, ɗan majalisa mai wakiltar shiyyar Haɗeja, Alhaji Abubakar Jallo cewa ya yi Badaru ya haifi ‘ya’ya kuma ‘ya’yan sun gaji ubansu wajen tsefewa da tsantseni da kiyaye dukiyar gwamnati.

Ya kuma buƙaci matasan su mara wa Gwamna Badaru baya domin ƙasar nan tana buƙatar mutane irinsa wajen jagorancin ƙasar, kasancewar mutum ne mai tausayi da tsoron Allah. 

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamna Badaru Abubakar na jihar ta Jigawa, ya ce a yau farin cikin sa ba ya misaltuwa har ma yana jin ba zai iya barci ba, saboda farin ciki.

Saboda haka ya buƙaci su zama masu haƙuri da juriya a kodayaushe ancikin harkokin siyasa dankuma na rayuwar yailu da kullum.

Gwamna Badaru ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya na haɗa wa sassan jihar da tashar jirgin ƙasa, ya ce hakan ba ƙaramin ci gaba ba ne ta fuskar tattalin arzikin ƙasa.

Ya kuma gode wa Shugaba Buhari game da bai wa mutanen jihar Jigawa mutum 167,000 tallafin Naira dubu biyar-biyar a duk wata da suke amfana domin rage raɗaɗin rayuwa.