Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu gungun ’yan ta’adda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a rukunin gidaje na Gwarinpa, wanda shi ne rukunin gidaje mafi girma a babban birnin tarayya, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna.
Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun kai farmaki ne a safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022 tsakanin ƙarfe 1 na safe zuwa 4 na safe.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ’yan bindigar da ke da yawan gaske suna ɗauke da wuƙaƙe da adduna, suna shiga gida-gida cikin rukunin gidajen.
Ya ci gaba da cewa, da yadda suka gudanar da aikin a yankin, an yi garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ya ci tura a lokacin haɗa wannan rahoton, amma tuni wasu jami’an ’yan sanda suka isa wurin da lamarin ya faru.
Wannan harin na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da ’yan Nijeriya suka shiga cikin kaɗuwa sakamakon harin da aka kai cocin St Francis Catholic Church a garin Owo, jihar Ondo a ranar Lahadi, inda aka kashe masu ibada da dama.