Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar ci gaban Irigwe (IDA) ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mutane 14 a wani hari da suka kai da tsakar dare ranar Lahadi a ƙauyen Ri Do, wanda ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato, inda mafi yawan mazauna ƙabilar Irigwe ne ke zaune.
A wata sanarwa da ƙungiyar IDA ta fitar ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Sam Jugo, ta bayyana cewa bayan samun labarin harin, ƙungiyar ta aika da wani wakilinta don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ya ce sun tabbatar da cewa an kashe mutane 14, yayin da wata mata mai suna Linda Moses mai shekaru 32 ta ji munanan raunuka, kuma a take aka fara ba ta kulawa.
Kungiyar ta yi kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro don hana sake aukuwar irin wannan hari ko ramuwar gayya.
Har ila yau, sun bayyana cewa suna fatan hukumomi za su ɗauki matakin da ya dace yayin da al’ummar ke shirin birne gawarwakin waɗanda suka rasa rayukansu.
