‘Yan bindiga sun sace shugaban APC a Neja

Bayanai daga yankin ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja, sun nuna ‘yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na ‘Zonne C’, Aminu Bobi.

Binciken MANHAJA ya gano cewa an yi gaba da Bobi ne a lokacin da ya je duba masu yi masa aiki a gona a ranar Asabar da ta gabata.

Wata majiya ta kusa da wanda lamarin ya shafa ta ce, ‘yan bindigar sun kai hari a gonar ne a kan babura inda kowane babur ke ɗauke da mutum uku, sannan suka yi ta harbe-harben bindiga a iska.

Majiyar ta ƙara da cewa Bobi ne kaɗai ‘yan bindigar suka ɗauke amma ba su taɓa ko mutum guda ba daga ma’aikatan da ke aiki a gonar a lokacin harin.

Ya zuwa haɗa wannan labari, duk wani ƙoƙari da aka yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar, hakan ya ci tura.