‘Yan bindiga sun sake kashe lauya a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun kashe wani lauya mai suna Barista Ahmad Muhammad Abubakar a Jihar Zamfara.

Majiyarmu ta ce ‘yan bindigar sun bi margayin ne har gidansa da ke garin Kwatarkwashi, cikin Ƙaramar Hukumar Bungudu suka hallaka shi.

Kafin rasuwarsa, marigayi Muhammad shi ne sakataren walwala na Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen Gusau.

Kazalika, shi ne ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a mazaɓar Bunguɗu ta Yamma ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP a yayin babban zaɓen da ya gabata.

Duk da dai Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara ba ta ce komai kan batun ba, sai dai majiya ta kusa da marigayin ta tabbatar da faruwar hakan ga jaridar News Point Nigeria.

A cewar Aminu Lawal Bungudu, “Bayan da ‘yan bindigar suka shiga gidan suka haɗu da matar gidan a lokacin da take ƙoƙarin shiga ban-ɗaki, a nan suka farmake ta, inda ita kuwa ta saka ihun neman taimako, a wannan lokaci mijinta ya ji ihun nata ya fito.

“Daga nan suka kama mijin suka tafi da shi, a hanya suka kashe suka bar shi cikin jini,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ba su da tabbacin ta yaya suka kashe shi, kawai dai sun tsinci gawarsa ne a hanya.

Idan ba a manta ba, a baya makamancin wannan ya faru a watan Agustan 2022 a jihar, inda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe Barista Benedict Torngee Azza a Gusau, babban birnin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *