‘Yan bindigar da su ka sace mahaifiyar Rarara sun ce a biya Naira miliyan 900

Spread the love

Daga YUSHAU A IBRAHIM

Waɗanda suka yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara sun ce a bada Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa don sako ta.

Wani makusancin ahalin, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa ƴan bindigar da farko sun ce Naira biliyan 1 za’a biya, daga baya kuma sai suka rage miliyan 100 a wata hirar waya da aka yi da ɗaya daga cikin iyalanta.

Bayan garkuwa da ita ne, Rarara ya fara rashin lafiya, don haka sai suka amince da tattauna da wani daga cikin ƴan gidan inda suka ce Hajiyar tana cikin ƙoshin lafiya kuma ana biyan kuɗin za su sako ta.

Wakilin tattaunawar da ƴan bindigar, ya kara da cewa tun daga nan basu sake kira ba, amma sun jiran kira na gaba domin cigaba da tattaunawa.

Sannan, ya ƙara da cewa, garkuwa da aka yi da ita, abu ne wanda aka shirya shi, domin sun zo da hoton Hajiyar ne don kar su yi garkuwa da wacce ba ita ba.

Bayan haka ne, mutane a ƙauyen Kahutu su ka shiga damuwa domin matar ta kasance mai kirki ce saboda irin taimakon da take yi wa al’ummar yankin.

By Babaji