Gwamnatin tarayya ta yi nasara kan gwamnoni akan cin gashin kan ƙananan hukumomi

Spread the love

Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Binciken Kuɗaɗen Najeriya (NFIU) sun yi nasara a shari’ar da suka shigar kan gwamnonin jihohi game da cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Alƙalin Kotun Tarayya Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da hukunci ranar Litinin, 24 ga watan Yuni 2024, inda yake bayyana nasarar gwamnatin tarayya a shari’ar.

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta kai gwamnatin tarayya ƙara da NFIU saboda shiga cikin ikon gwamnatocin akan Ƙananan Hukumomi, suna nuna hujjoji daga kundin tsarin mulkin 1999.

Sai dai NFIU sun fitar da sabbin ƙaidoji, wanda cikin su shine rage fitar yawan kuɗi daga asusun kananan hukumomi zuwa naira dubu ɗari biyar a kowace rana.

Shugaban NFIU ya ce, “Daga wannan hukunci da kuma daga yau, za a bayyana duk ayyukan da suka shafi kuɗaɗen Kananan Hukumomi ga ICPC da EFCC baki ɗaya.

By ukarofi