Matar mataimakin gwamnan Jihar Niger, Garba Yakubu ta rasu ranar Talata a garin Minna.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ummikaltumi Kuta ta tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa Hajiya Zainab ta rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnan Jihar Niger,Umaru Bago ya nuna alhinin sa ga mutuwar. Inda ya bayyana cewa mutuwar Hajiya Zainab a matsayin rashi ga duk al’ummar Jihar Niger. Kamar yadda sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Ibrahim Bologi ta bayyana.