Daga AMINA IBRAHIM
Manhajar Tapswap wacce ɗaya daga manyan kafofin ‘Blockchain’ ce ta ce ta dakatar bada lasisin shiga zauren cinikayya ga masu amfani da ita.
Tapswap dai ya samu karɓuwa a cikin ƴan Nijeriya inda a yanzu haka aƙalla mutane sama da miliyan 50 ke amfani da shi tun ƙaddamar da shi a watan Fabrairun 2024.
Hukumar kula da manhajar ta ce ta dakatar lasisin cinikayyar ne da aka tsara zai da fara aiki daga 1 ga watan Yuli domin sauƙaƙe wa masu amfani da shi a zango na uku bisa huɗu.
Ta kuma ƙara jaddada ƙoƙarinta na inganta manhajar da kuma da kuma samar da yalwataccen bayanin lasisin cinikayyar ta yadda za a ƙaddamar da shi ta hanyar da ta dace.
Zuwa yanzu dai, ba a sanar da lokacin cigaba da bada lasisin cinikayyar ba har sai an kammala aikinsa, kamar yadda jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito.