
Daga SANI NURA
Ƴan bindiga sun kashe wani malamin jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma da ke jihar Katsina.
Malamin, mai suna Dakta Gyan David wanda shi ne shugaban tsangayar tattalin harkar noma da raya karkara, an kashe shi ne da asubahin ranar Talata da misalin ƙarfe 1:30 a gidansa da ke unguwar rukunin gidajen Low-Coast yayin wani sabon hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.
Jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito cewa, ƴan bindigan sun shigo yankin ne da wasu muggan makamai inda suka yi ta harbe-harbe domin su tsorata mutane, sannan sun kuma yi garkuwa ƴaƴan malamin biyu.
Mai magana da yawun ‘Yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq ya ce sun tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce za su fitar da cikakken jawabi a kai.
Dutsinma na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 10 a Katsina da a fama da rashin tsaro inda a kwanakin nan ne a ke kai hare-hare akai-akai duk da ƙoƙarin gwamnatin jiha da kuma hukumomin tsaro.
