’Yan bindigar Zamfara sun fara kai samame gida-gida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A halin yanzu matsalar ’yan bindiga a Jihar Zamfara ta sake sabon salo, inda a kullum ake samun rahotannin kai farmaki kan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba har a gidajensu.

Binciken da manema labarai suka gudanar ya nuna cewa, a yanzu ’yan bindigar sun canja sabon salo zuwa shiga gida-gida suna kai hare-hare cikin gaggawa kuma babu ƙaƙƙautawa.

Sai dai a ranar Larabar da ta gabata ne ’yan bindigar suka kai farmaki ƙauyen Yanbuki da ke ƙaramar hukumar Zurmi, inda suka kashe mutane bakwai tare da sace shanu da tumaki kusan 15,000.

Wani ɗan ƙauyen da abin ya faru mais una Garba Musa ya shaida wa manema labarai cewa, ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne a daren ranar Talata, inda suka yi ta harbi ba ƙaƙƙautawa.

Musa ya ce, “daga isarsu suka buɗe wuta ga duk wanda suka gani, sauran mutane kuma suka arce don neman mafaka. Daga baya sun koma shiga gida-gida, suna neman kayan abinci da dabbobi sannan kuma sun fasa shaguna da dama. Sun kuma yi awon gaba da dabbobin gida sama da 1,500 kamar shanu, tumaki da awaki.”

Ya ƙara da cewa, bayan ‘yan bindigar sun bar ƙauyen ne mazauna garin suka fito daga mavoya, inda suka gano cewa an harbe mutum bakwai har lahira, yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

“Mun binne mutane bakwai, amma adadin waɗanda suka mutu zai iya zarce haka saboda wasu mutane sun gudu zuwa daji kuma har yanzu ba a gansu ba,” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ƙara da cewa, “tuni kwamishinan ‘yan sandan ya baza jami’an ‘yan sanda isassu a yankin domin a samu zaman lafiya.”

Kodayake, an lura da cewa, an ɗan samu tsagaitawa kwanan nan bayan da aka ƙaƙaba takunkumin hanyoyin sadarwar na wayar tarho zuwa a wurare, saboda rahotanni sun nuna cewa, ‘yan bindiga su na yin amfani da ‘yan leƙen asiri da masu bayar da labari da ke zaune a cikin al’ummomi.