Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Malama Hafsat Saidu, mahaifiyar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi masu haƙar ma’adinai, waɗanda suka mutu a Jihar Neja, ta ce a baya ta taɓa shafe kwanaki biyar a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) bayan jami’an hukumar sun kama ta a wani wurin haƙar ma’adinai.
NSCDC ta ce, a ranar Alhamis cewa an kama waɗanda ake zargin ne yayin wasu samame da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankin Lt. Gen. Mohammed Inuwa Wushishi Estate, da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.
Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, ya ce a cikin wata sanarwa cewa “an samu gawawwakin mutane da dama daga cikin waɗanda ake tsare da su a farkon safiyar Alhamis, sakamakon zargin ɓarkewar wata cuta.”
Bayan faruwar lamarin, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan yadda mutanen suka mutu.
A wata hira da TheCable ta yi da ita da harshen Hausa, Saidu ta ce ta biya naira 45,000 kafin a sake ta daga tsarewar.
Ta ƙara da cewa, an kama ta ne bayan jami’an NSCDC sun kai samame wurin haƙar ma’adinai, lamarin da ya sa ma’aikatan wurin suka gudu.
Mahaifiyar, wadda ke cikin jimami, ta ce a baya jami’an hukumar sun taɓa kama ta, inda ta shafe kwanaki biyar a tsare.
“Ba su taɓa kama ’ya’yana ba sai yanzu, amma a baya sun kama ni. Na shafe kwanaki biyar a ɗakinsu na tsarewa. Mun roƙe su a ba ni beli, amma suka ƙi,” inji ta.
Ta ce a lokacin da take tsare, ’ya’yanta sun riƙa kawo mata abinci. Saidu ta ce, daga bisani ta nemi taimakon wani babban jami’in NSCDC domin a sake ta bisa tausayi. Ta ce, an kuma karɓi naira 10,000 daga wata mata da aka tsare tare da ita, inda daga ƙarshe aka biya jimillar naira 45,000 kafin a sake su.
Ta ce, “ ’Ya’yana sun kasance suna yawan zuwa hanya suna kawo min abinci a ɗakin tsarewar. A rana ta biyar, na gana da ɗaya daga cikin shugabanninsu, wanda Bahaushe ne ba, ɗan Yarbawa ne. Na gaya masa ina da ’ya’ya da jikoki, na roƙe shi ya taimaka a ba ni beli… Ya ƙi, har ma ya ture ni da ƙafarsa a lokacin da nake riƙe da ƙafafunsa ina roƙonsa. Mun bi shi har zuwa motarsa kafin daga ƙarshe ya amince. Ya ce dole mu biya naira 10,000 na beli, sannan a ƙara naira 5,000 ga wanda zai bi ni domin tabbatar da gidana. Wata matar da aka tsare tare da ni kuma an ce ta biya naira 10,000. A ƙarshe, sun karɓi naira 45,000 daga hannunmu kafin su sake ni. A wancan lokacin da suka kama ni, zinaren da nake da shi bai wuce naira 3,900 ba, amma na shafe kwanaki biyar a wurin.”
Saidu ta kuma bayyana yanayin da ta ce suka fuskanta a lokacin da take tsare, inda ta yi zargin cewa an tilasta musu kwana a wurin da suke yin fitsari. “Mun kasance muna kwana a daidai wurin da muke yin fitsari. Sai mun yi amfani da tabarmarmu wajen rufe fitsarin, sannan mu kwanta a kansa. Tun daga lokacin da aka kama mu, ba mu sake yin salla ba,” inji ta.
Ta ce, daga cikin ’ya’yanta ma an kama su, amma mutum ɗaya kacal ne ya tsira. A cewarta, daga baya aka sanar da ’yan uwa cewa mutanen da aka kama sun mutu. “Sun kama yaran nan suka cika motarsu da su. ’Ya’yana suna cikinsu, kuma mutum ɗaya ne kawai ya tsira,” inji ta. Lokacin da muka kai masa abinci, sai aka gaya mana cewa ya mutu, kuma wasu mutane da dama ma sun mutu.”
Saidu ta musanta iƙirarin cewa sinadarai da aka yi amfani da su a wurin haƙar ma’adinai ne suka haddasa mutuwar mutanen. Maimakon haka, ta yi zargin cewa sinadaran sun shafi mutanen ne a cikin ɗakin tsarewar NSCDC da aka ajiye su. Ta ce ɗanta ya gaya mata cewa an fesa wani abu mai kama da maganin sauro a cikin ɗakin, sannan aka rufe ƙofar nan take.
“ɗana ya ce an fesa wani abu mai kama da maganin sauro, kuma nan take bayan an fesa shi, sai suka rufe ƙofar ɗakin. Makogwaronsu suka fara bushewa, har ɗaya daga cikinsu ya tilasta shan fitsarinsa,” inji ta.
Ta ce, daga baya mutane sama da 30 suka mutu, tana mai kira ga gwamnatin jihar da ta shiga cikin lamarin. “Wannan abu bai taɓa faruwa a Jihar Neja ba. Ba mu yarda da wannan bayanin ba,” inji Saidu. Mun gaya musu cewa sun kashe mutanenmu kuma dole ne a yi mana adalci.”
Saidu ta kuma yi zargin cewa sojojin da suke wurin sun umarci masu zanga-zangar su bar wurin lokacin da suka yi ƙoƙarin ganawa da Gwamnan Jihar Neja. Ta ce, “Sojojin da suke wurin sun umarce mu da mu tafi ko kuma a kama mu. Lokacin da muka dage cewa muna son ganin gwamna, suka gaya mana cewa ba za a bar mu mu gan shi ba, kuma idan ba mu tafi ba, za a kama mu.”
Saidu ta ce iyalan waɗanda abin ya shafa na cikin mawuyacin hali na rayuwa, saboda wasu daga cikin waɗanda suka mutu su ne ke ɗaukar nauyin iyalansu. “Na rantse da Allah, a yanzu ba mu da abin da za mu ci. A gaskiya, a wannan lokacin ina nan ina neman duk wani aikin da zan samu domin mu sami abin da za mu ci,” inji ta.
