‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ƴan sanda a Katsina sun sami nasarar daƙile harin ƴan bindiga a ƙauyen Ɗorawa a ƙaramar hukumar Dutsinma.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata takardar sanarwar da ya fitar.
Ya bayyana cewa yan bindiga ɗauke da manyan makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 sun kai hari a kauyen Ɗorawa sai dai basu sami nasarar ba bayan da jami’an tsaro suka shiga ƙauyen akai ta ɗauki ba daɗi da ƴan bindigan.
DSP Abubakar yace ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun samu nasarar kashe yan bindiga su shida wasu kuma sun gudu da raunuka .
Ya ƙara da cewa ƴan sandan su sami maido da shanu guda 61 da ƴan bindigan suka gudu suka bari a ƙauyen.
“Sauran dabbobin da ƴan sanda suka maida sun haɗa da Raunana 44 da Jakuna biyu tare da kare ɗaya”inji DSP Abubakar Sadiq.
Kwamishinan ƴan sanda CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba da irin ƙwarewar aiki da jami’an tsaron suka nuna wajen yaƙar yan bindiga a ƙauyen.
CP Aliyu ya kuma jaddada ƙudirin rundunar ƴan sanda a jihar na tabbatar da tsaro da kawo zaman lafiya a jihar.