’Yan sanda sun kama ƙusa a NNPP bisa zargin sukar Gwamna Zulum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta kama wani jigo a jam’iyyar NNPP, Atom Magira, bisa zargin sukar Gwamna Babagana Zulum.

Hadimin Mr. Magira, Mohammed Yahaya, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun ɗauke shi ne a daren Lahadi.

Manhaja ta rawaito cewa Magira, wanda ya taɓa neman takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2019, yana daga cikin manyan ‘yan adawa a jihar. Ya kasance mai magana sosai kan wasu manufofin Gwamna Babagana Zulum.

Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an kama Mr. Magira ne saboda wani allon talla da magoya bayan “YES TO MERGER” suka ɗauki nauyi, suna kira da a haɗa kan dukkan jam’iyyun siyasa a jihar.

Allon da aka rubuta “Say Yes To Merger” tare da hoton Mr. Magira daga baya an lalata shi ba tare da sanin wanda ya yi hakan ba.

“Gwamnatin jiha ce ta bayar da umarnin, ba sa son ganin wata babbar adawa a jihar. Duk wanda ya yi hakan za a takura masa, hakan ya zama ruwan dare tun daga 1999, amma Magira ya ci gaba da kasancewa mai kawo adawa mai ma’ana a Jihar Borno,” inji wata majiya.

“Har yanzu Magira yana tsare a safiyar Litinin, amma ba a tabbatar ko za a gurfanar da shi a kotu ba,” wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ta ce wa wakilinmu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Borno, Nahum Kenneth Daso, ba  a samu jin ta bakin sa ba kan lamarin.

By ukarofi