‘Yan sanda sun kama mutum 28 bisa zargin kashe Shugaban Ƙasar Haiti, Moïse

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Sandan Ƙasar Haiti sun kama wasu mutum 28 dukkansu baƙi da aka yi zargin suna da hannu cikin badaƙalar kashe Shugaban Ƙasar, Jovenel Moïse, a farkon wannan makon.

Bayanan ‘yan sandan sun nuna cikin waɗanda aka tsaren wasunsu sun taɓa yin aikin soja, kuma an kama yawancinsu ne bayan ɗauki ba daɗin da aka da aka yi na musayar wuta a wani gida da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar.

An gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai jina-jina a ran Alhamis da ta gabata tare da wasu makamai da aka samu aka ƙwace a hannunsu.

‘Yan sandan ƙasar sun ce sauran mutum takwas da ake zargi har yanzu ana kan neman su, yayin da kuma aka samu nasarar harbe wasu mutum uku daga ciki har lahira.

Da sanyin safiyar Larabar da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka kutsa kai cikin gidan Shugaban Ƙasar a Port-au-Prince, inda suka harbe shi da matarsa. An samu Mista Moïse kwance kuma a mace ɗauke da raunukan harbin bindiga har guda 12 a jikinsa wanda bayanan tsaro suka nuna a nan take ya mutu.

Haka ma matar marigayin, Martine, ta ji mummunan rauni sakamakon harbin da aka yi mata wanda hakan ya sanya aka tafi da ita zuwa Florida don neman magani.