Abinda ya haɗa ni rigima da Baturen ‘Yan Sandan Hotoro – Mansurah Isah

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A sati biyun da su ka gabata ne tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta yi wata sanarwar ɓatan wata yarinya wadda har ta zargi Baturen ‘Yan Sanda na Hotoro da cewar ya na neman ya ɓoye gaskiyar abin da ya faru, kuma hakan ya sa maganar ta yi tsayi har ta je ga ofishin Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano. Don haka ne muka nemi jin ta bakin Mansurah Isah don jin yadda maganar ta samo asali. Wakilin Manhaja a Kano ya samu damar tattaunawa da Mansura don kawo wa masu karatun mu gaskiyar zancen, domin an ce waƙa a bakin mai ita tafi daɗi:

Mun samu labarin wata matsala ta vatan yarinya a kwanakin baya da ki ka sanar tare da yin ƙorafin ana neman a danne maganar. Ko ya ya abin ya faru?
To abin dai da ya faru shi ne ranar Alhamis 2/7/2021 da misalin ƙarfe 6 na yamma sai yayana Malam Sani ya kira ni ya ke sanar da ni cewa ba a ga ‘yar sa ba wata ƙaramar yarinya ce mai suna Mama. Sai na tambaye shi me ya faru? Ya ce shi ma bai sani ba, yanzu shi ma aka kira shi aka faɗa ma sa, kuma a lokacin tun ƙarfe biyu ba a gan ta ba, har ma na ke cewa, me ya sa tun lokacin ba a ɗauki wani mataki ba. Sai kawai na tashi na nufi gidan na su da ke can ‘Ring Road’ a wata unguwa Walalamɓe, da na je sai Maman su ta ke faɗa mini ta fita daga gida ne ta bar su su na cin abinci da ‘yan’uwan ta ta je ta yi sayayya, ‘yan mintuna kaɗan sai ta dawo ba ta same ta ba, kuma ba wani lokaci mai tsayi ta yi ba a tafiyar ta, amma ta na dawowa sai ba ta same ta ba. To abin ma da ya fi tayar da hankali yaran ba sa fita, don haka ko a unguwar ma ba a san su ba ballantana ko wasu maƙota idan sun gan ta su gane ta, saboda kullum a gida su ke, don haka ma da muka fito muka fara neman duk wanda muka tambaya sai ya ce bai ga wata yarinya da alamar ta vata ba, da fari mun ɗauki abin da wasa, sai ya zama aiki sosai don har ƙarfe biyu na dare muna neman ta babu labarin ta gidajen masu unguwanni da Masallatai duk muka bada cigiyar ta, don mu a tunanin mu ta bi uwar ne da za ta fita kuma sai ta ɓace mata ta rasa hanyar dawowa, amma dai ba mu same ta ba haka muka haƙura muka ce sai da safe ma ci gaba.

Da safe muka ci gaba da neman yarinyar, muka je ofisoshin ‘Yan sanda na Hotoro muka bada sanarwa. Daga nan muka ci gaba da nema har zuwa tashoshin Mota don an ce wasu idan sun saci yara suna zuwa tasha su hau Mota su tafi da su. Duk wata tashar Mota mun je mun binca har cikin Motocin da aka yi wa lodi suna shirin tashi duk muka dudduba, muka tafi Hukumar Hisba, duk babu labarin ta har cikin dare muna neman ta. Lokacin dare ya fara yi kuma ga hadari sai hankalin mu ya ƙara tashi, muka fara duba kangwaye da nufin ko an kashe ta an jefar da ita mu samu gawar ta.

To muna cikin haka ne, sai aka kira Baban yarinyar aka ce an ga wata yarinya a wani gida da aka tsinta mu je ko ita ce, sai Baban ya tafi muka zauna muna addu’a, mu na jiran ya dawo ƙila an yi sa’ar samun ta. Cikin ikon Allah muna zaune sai kawai muka ji ihun mutane suna murnar an ga Mama, sai muka tashi muka fita muna murna kowa yana farin ciki. “

Ganin an same ta ba mu tsaya ba sai kawai muka tafi Asibiti domin a bincika lafiyar ta don mu samu nutsuwa kada daga baya kuma a samu wata matsalar ta ɓullo. To da muka ɗauki yarinya muka saka ta a mota sai kawai ta kama ihu ta na cewa ba na so. To da ya ke dare ne akwai duhu motar, sai muka kunna fitila, amma dai duk da haka ta ci gaba da yin ihun ta na haɗe ƙafafun ta, ta na cewa “ba na so” , da haka muka je wani asibiti mai zaman kan ta a nan Unguwar Badawa na samu likita na yi masa bayanin abin da ya ke faruwa. To da aka zo za a kwantar da ita a gadon asibitin sai yarinyar ta ƙi, ta na ta ihun ba na so. Sai likitan ta ce tun da ta na wannan ihun ba za ta bayar da damar a duba ta yadda ya kamata ba, domin akwai alamar wani da ya ke damun ta don haka sai an yi mata Allurar bacci za a samu damar duba ta sosai. kuma ana yi mata ba ta fi minti goma ba ta fara bacci.

Kuma wani abin da ya ba mu mamaki mun gan ta da kayan da ba da shi ta ɓata ba, wanda yanzu kayan su na wajen Hukumar ɓangaren masu binciken satar mutane. To da ta yi bacci ne aka fara duba ta, tun daga kan ta, wuyan ta, maƙogaro, zuwa hancin ta da bakinta zuwa cikin ta da gaban ta har zuwa ƙafa, ta ce duk babu komai.

Daga nan sai aka juya ta baya aka yi kamar yadda aka yi mata a gaban ta sai ta zo ɗuwawun ta in da ta ke kashi ta duba, sai ta ga ya yi ja, yana jini, don haka sai likitar ta ce da mu “Sai dai ku yi haƙuri, don yarinyar nan an riga an ɓata ta.” sai uwar ta fara kuka. Nace da ita ki yi haƙuri, yanzu da gawarta muka samu fa. Za mu san yadda zamu kula da ita yadda abin ba zai yi ma ta illa nan gaba ba. To muna cikin wannan sai likitar ta ce sai an yi mata gwaji na HIV, kuma aka je aka yi ma ta aka tabbatar da babu matsala, amma sai bayan wata uku za mu koma don mu ƙara tabbatarwa, domin yanzu ba zai iya nuna komai ba, sai aka ɗora ta a kan wasu magunguna, kuma ta ce mu je gida mu saka yarinyar a ruwan zafi mu rinƙa yi ma ta gashi, daga nan muka tafi gida.

A lokacin da likita ta ba ku wannan bayanin na halin da yarinyar ta ke ciki ku na da yawa a gurin?
Duk da mun je mu da yawa amma sai ba mu faɗa wa sauran ba, sai ni da Babar ta ne muka san abin da ya ke faruwa.
To washe gari sai ga wasu mata sun zo wai kayan da ya ke jikin yarinyar na ‘Yar su ne, sun zo su karɓa su bada nata. To sai abin ya ba mu mamaki, domin ga abin da ya faru ga yarinya, sai kuma wasu su zo su ce su ne su ka cire mata kayan jikin ta su ka saka mata wani. Abin dai sai ya ke nema ya zama rigima har suna cewa, su ‘yan jihadi ne su na ƙoƙarin za su yi kisa, kuma kayan da su ka saka wa yarinyar fa duk ya yi datti, ya koɗe. To wannan ya sa muka kai maganar ofishin ‘yan sanda na Badawa, su ka ce a je a ɗebo su a kawo su. Aka je gidan su aka taho da su , da aka kawo su ne aka karanta abinda ya faru, sai su ka ji abin ya na da tsayi kuma ga in da muka fara kai rahoton matsalar, don haka sai su ka ce za su mayar da maganar zuwa Hotoro don a can aka kai farkon maganar.

To da muka je Hotoro dare ya yi kuma sai aka ce Baturen ‘Yan Sanda na wajen ba ya nan sai dai mu dawo da safe. Kuma sai aka fara ɗaukar bayanan kowa, sai a cikin bayanin na su su ka ce su har qunshi su ka yi wa yarinya sun yi ma ta hotuna da Video.

Sai aka ce da su to ku mene ne na yi wa yarinya ƙunshi. Yarinyar da a ke nema ai gidan Mai unguwa ya kamata su kai ta, to wai sun kai ta gidan mai unguwa, kuma sai aka ga ta saba da wata yarinya Fatima, don haka aka ce su tafi da ita. Nan ma aka ce tun da Mai unguwa ya ba su me ya sa su ka bar ta a wajen su ba su kai ta wani Ofishin ‘yan sanda ba. Sai a nan su ka amsa kuskuren su. Har sai da mai rubuta bayanan ran sa ya ɓaci, ya ce ba ku bi tsarin da ya dace ba kun bar yarinya a hannun ku, kuma kun zo kuna maganar aba ku kayan da ku ka saka ma ta har ma kuna cewa za ku kashe mutum a kan kayan, sai kawai ya ce a saka su a bayan kanta, sai da safe idan Baturen ‘Yan Sanda ya dawo. To da safe aka ce mu dawo goma, ni kuma na je wani wajen ban zo da wuri ba. Shi Baban yarinya shi ya fara zuwa wajen, sai kawai na ji ya kira ni ya ce na yi sauri na zo don ana neman a kori maganar. Don bai bari ma na yi magana ba.

Sai kawai na tafi na je na same shi muka gaisa na ce da shi, don Allah maganar yarinya ne da muka kawo. Sai kawai ya hau ni da faɗa yana cewa, “to sai menene? Me ya faru? Kuna yi wa mutane sharri.”

Sai na ce Yallaɓai ka saurari maganar mu mana, sai kawai ya ci gaba da magana ta in da ya hau ba ta nan ya ke sauka ba, ya na ta zagi ‘yar Bura’uba, ‘yan isaka, babu irin zagin da bai mana ba, muka ce so bai kamata ka bi wani ɓangare ba sai na matso kusa da shi ina so mu yi maganar don kada mutane su ji abin da ya ke faruwa, sai kawai ya rinqa ɗaga murya ya na cewa “ƙarya ne sharri ku ka yi musu”.
Sai na ce har asibiti muka je aka tabbatar, sai ya ce “ƙarya ne kun haɗa baki da likita ne. Sai ya kira wata ‘yar Sanda ya ce da ita ta tafi asibitin gwamnati ta yi gwajin ba za mu yarda da na asibiti mai zaman kan ta ba. Sai na ce to wanne asibitin za mu je?


Sai ya ce “ke wa ce ce da za ki tambaye ni asibitin da za a je? ke za ki gaya mini aikin da zan yi. ‘yan iska karuwai.
Sai kawai na fusata na ce” To menene na zagi na kuma har ka ce da ni karuwa, to idan ka ƙara faɗa mini sai na nemi haƙƙi na. Daga nan kawai sai ya kira yaran sa maza su ka ɗauke ni da ƙarfi su ka fitar da ni. Kuma ya ce idan na sake zuwa kada a bar ni na shigo.

Wannan ya sa ni kuma na ce ko dai ka yi abin da ya dace, ko kuma mu san duk wata hanyar da za mu bi don mu samar wa da yarinya ‘yancin ta. Shi ne ya ce ke wa ce ce. Idan kin isa ki je ki yi abin da za ki yi. Sai na ce Ni babu abin da zan yi don kana gaba da ni, amma ina da hanyar da zan bi na samar wa da yarinya ‘yancin ta. To shi ne aka ga na saka abin a Soshiyal Midiya.

Ko kun sake koma wa asibiti kamar yanda ya buƙata?
Mun koma, shi ne muka tafi asibitin Nassarawa aka yi gwaje gwaje aka ce mu koma washe gari zuwa Ofishin ‘yan sanda, to ni kuma sai na je na kai maganar barazana da Baturen ‘Yan Sanda na Hotoro ya yi mini zuwa ofishin Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano. Saboda ya kore ni daga gida na, don ofishin ‘Yan Sanda gida na ne a matsayi na na ‘yar ƙasa, ya kore ni, ya ce kada na ƙara zuwa, kuma gidan mu ne a nan za a share mana hawayen mu don haka za mu je duk lokacin da ta kama ba tare da an hana mu ba, don dokar ƙasa ce ta ba mu dama don haka na kai koke na a wajen Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano na rubuta takardar koke na shigar.

To kafin mu ƙaraso ina jin an ba shi labarin zuwan na mu don haka kafin takardar tawa ta kai wajen Kwamishina shi ya riga ya kai ƙara ta ofishin Hukumar tsaron ƙasa CID ya na neman haƙƙin sa wai na ce ma sa shi mai garkuwa da mutane ne, kuma ya na soyayya da mata masu garkuwa da mutane.

To sai aka kira ni kafin tawa ƙarar ta je wajen Kwamishina. Da na je sai aka ce a yi maganar abin da ya faru. A gaban su, sai shi wannan mutumin ya ce ai shi bai kore ni ba. Kuma ana cikin haka sai ga lauyan sa, a she har ya shigar da lauya cikin maganar, sai na ke cewa da shi a matsayin ka na Baturen ‘Yan Sanda menene na zuwa da lauya. In kana da gaskiya ka faɗa.

Sai aka tambaye ni mene ne shaida ta da na ce ya kore ni. Na ce ina da ita, don ko yaran sa su na nan don su su ka fitar da ni, kuma na yi Video ɗin wasu ma a waya ta, kuma in ƙarya na ke yi masa a je a yi bincike. To da lauyan sa ya zo, sai ya ce ka ce ka kore ta.To sai ya amsa cewar ya kore ni. Sai aka ce menene dalilin da ya sa ya kore ni? Sai ya ce ai ta zage ni. To ni kuma sai na ce “Yanzu saboda Allah zan je har ofishin sa na zage shi amma yaran sa su bar ni ba tare da an kulle ni ba, har ya ce a kore ni daga ofishin sa.

To daga nan sai aka ce mu rubuta bayanan mu ni da shi, kuma aka karɓi wayoyin mu. Daga baya dai an yi mana sulhu aka daidaita mu, yanzu babu wata matsala a tsakanin mu da shi. Kuma maganar waccan yarinyar a yanzu ta na wajen Jami’an tsaro masu bincike a ɓangaren masu garkuwa da mutane, don haka binciken su ne zai tabbatar da abin da ya faru. Muna nan dai muna jira.

To madalla, mun gode.
Ni ma na gode.