‘Yan sanda sun kama mutum huɗu da hannu a harin Fadar Sarkin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama mutane huɗu da ake zargin su da hannu a tada rikicin da aka yi a Fadar Sarkin Kano a ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya aika wa manema labarai, inda ya ce a halin da ake ciki jami’ai suna gudanar da bincike akan su.

Ya bayyana cewa, Kwamishinan ƴan sandan, Ibrahim Adamu Bakori ya kafa tawagar bincike game da lamarin, wanda ya auku tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 15, Muhammadu Sanusi na II.

A ranar Lahadi ne aka samu rikici a tsakanin ɓangarorin biyu, a lokacin da Sarki Aminu Ado ya fito daga gidansa da nufin tafiya Fadar Nasarawa, inda ya bi ta hanyar Ƙofar Kudu.

Lamarin da ya sa rikicin ya ɓarke, inda aka raunata masu gadi da ƙone motocin ƴan sanda.

By Babaji