Ƙungiyar Bura-Pabir ta buƙaci a kafa Jihar Savanna a Kudu maso Gabas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar al’ummar Bura-Pabir ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta fara aiki akan takardar buƙatar kafa Jihar Savanna kamar yadda al’ummar yankin tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas suka buƙata.

Masu neman a samar da jihar suna ganin yin hakan zai taimaka wajen haɗe mutanen yankin da ƴan uwansu barebari, waɗanda a shirye suke su ba su goyon baya a siyasance da ci-gaba.

Dakta Yawutama Emmanuel Amaza shi ne wanda ya samar da ƙungiyar ta ‘Bura-Pabir Network’ da nufin fafutukar samar wa al’ummrsu jiha.

A lokacin da ya ke magana game da ƙudirin, Reberen Hon. James Pelachiroma ya yaba wa majalisa (Dattawa) ta 10 da masu ƙoƙarin samar da jihar bisa hoɓɓasa da suke yi wajen hakan ya tabbata.

Ya kuma ce, tun shekaru 40 da suka gabata ake fafutuka a kai, wanda sai yanzu batun ya yi ƙarfi akan lokutan baya da ake tattaunawa a kai.

Bura-Pabir, babbar ƙabila ce a Kudancin Jihar Borno daga cikin ƙabilu 35 ko makamancin haka dake yankin.

By Babaji