Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haɗin gwiwa na jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 30 a ƙauyukan ƙaramar hukumar Faskari.
Jami’an tsaron da su ka haɗa da sojojin ƙasa da na sama da kuma ‘yan sanda sukai artabu da ‘yan bindigan a ƙauyukan kadisau,Raudoma da Sabon Layi na ƙaramar hukumar Faskari.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya sanar da haka a wata takarda ɗauke da sa hannun sa .
Jami’an tsaron sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga 30, wasu sun gudu da munanan raunuka.
Suma ɓangaren jami’an tsaron ‘yan sanda uku sun mutu sai kuma sojoji biyu sun sami raunuka.
‘Yan sandan da suka mutu sun haɗa da sufeto Suleiman Ibrahim, sufeto Ibrahim Bello Bala da kofur Mohammed Lawal
Dr Mu’azu Ɗanmusa ya miƙa ta’aziya a madadin gwamna Dikko Raɗɗa da gwamnatin jihar Katsina.,
Ya bayyana sojojin da suka rasu a matsayin jajirtattu da suka sadaukar da rayukansu wajan kare rayukan al’umma.
Yanzu haka sojojin da suka samu raunuka na asibiti suna samun kulawa.
