‘Yan sanda sun musanta rahoton fashewar bom a tashar lantarki ta Zungeru

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

‘Yan sanda a jihar Niger sun ƙaryata waɗansu rahotanni da ke cewa an samu tashin bom a tashar wutar lantarki na Zungeru da ke jihar Niger inda suka ce labarin ba gaskiya ba ne.

Mai magana da yawun rundunar, Wasiu Abiodun ya ce labarin wanda ke yawo a kafafen yanar gizo, ƙanzon kurege ne da jama’a ya kamata su ƙi amincewa da shi.

Abiodun, ya ce babu wani abu mai kama da haka a tashar lantarkin, don haka jama’a su yi watsi da shi.

Ya kuma ƙara jaddada wa al’umma cewa, tashar tana gudana yadda aka saba ba tare da wani tseko ba, don haka su ke tantance da kuma tabbatar da sahihancin labari kafin amincewa da yin aiki da shi.

By Babaji