Wani otel ya rushe da mutane ciki a Abuja

Mutane da dama ake tunanin suna cikin ginin lokacin da bene mai hawa huɗu ya rushe a Abuja. Benen wanda yake jingine da Westbrook Hotel, yana garki a babban birnin tarayya Abuja.

Ana zargin shi otel ɗin Westbrook mallakin wani tsohon gwamna ne daga cikin jihohin Yammacin Najeriya.

Wani shaidar gani da ido, ya shaida cewa, yace lamarin zai iya haddasa a jikkata sosai domin ya hangi an ciro mutum biyu an tafi dasu asibiti. Akwai yiyuwar akwai sauran mutane sosai inji shi.

Sauran bayanai za su biyo baya.