Kotu ta buƙaci EFCC ta biya tarar Naira miliyan 3 kan shelanta kama matar Emefiele ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga HAMZA RUFA’I

Wata babbar kotu a jihar Lagas ta ce ba daidai ba ne shelanta neman kama matar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, Margaret da hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da laifukan da su ka shafi kuɗi (EFCC) ta yi.

Mai Shari’a, Deinde Dipeolu ya faɗi hakan bayan da Magaret Emefiele ta shigar da ƙara kan EFCC da a bi mata haƙkinta inda kotun ta buƙaci hukumar da ta biya tarar Naira miliyan uku ga daƙile ƴancin matar.

Magaret, ta shigar da ƙarar ne ganin yadda hukumar ta wallafa hotunanta a shafukan EFCC ba tare da wani umarni daga kotu ba, don haka ta ce tana so a bi mata haƙkinta.

Matar, ta kuma buƙaci kotun cewa ta umarci hukumar da ta cire hoton ta a jadawalin waɗanda ake nema tare aika saƙon bada haƙuri a gare ta a gidaje biyu na telebijin na ƙasa da kuma gidajen jaridu uku.

A hukuncin da kotun ta yanke makon da ya gabata, Mai Shari’a Dipeolu ya ce EFCC ta yi laifi kan buga hotun matar a jadawalin masu laifuka wanda hakan ya saɓa ma dokar sakin layi na 41 da na 42 na dokar adalci kan laifukan sata ta shekarar 2015, don haka za a biya tarar Naira miliyan 3 ga Matar kan daƙile mata ƴancinta.

By Babaji