Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Makamashi, musamman na man fetur da gas da dukkan sauran dangoginsu da kuma mabiyansu, wato ma’adanai waɗanda sun doshi sama da 50, su ne ruhin Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da kuma walwala, amma idan babu wata magana tartibiya daga mahakunta, shugabanni, game da wannan ruhi na ƙasa, babu abinda zai haifar illa ruɗani.
Kace-nace da ke faruwa dangane da tallafin man fetur tun daga ranar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya furta dakatar da bayar da wannan tallafi ga masu hada-hadar wannan haja da duniya ke buƙata, al’amura suke ta faruwa. Misali; hauhawar farashin kayayyakin more rayuwa nan da nan sai talauci ya kunno kai sai yunwa ta biyo baya tare da sauran fituntunu.
Idan yau ka ji Shugaban Ƙasa ya jaddada kalamansa na “no going back on petroleum subsidy”, wato dai babu sauran wani rangwame dangane da wannan makamashi na man fetur, duk da haka sai ka ji ta bakin wasu kafofin yaɗa labarai masu zaman kansu da kuma na sada zumunta suna ta yaɗa cewa, gwamnati na biyan maƙudan kuɗaɗe na tallafi, sai kuma daga bisani gwamnatin ta fito ta ce wannan magana ‘zuƙi ta malle ce’, kamar yadda ya faru a makon da ya gabata da ake yaɗa cewa, gwamnati ta yi “shirin kashe Naira tiriliyan biyar da biliyan huɗu kan biyan tallafin fetur”, daga baya sai mu ka ji ta bakin mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkoki yaɗa labarai, Bayo Onanuga, cewa, wannan magana “zuƙi ta malle ce”.
Tambayarmu ga Mista Bayo; idan ba rami, mai ya kai har aka yi wa makaho gargaɗi da ya kula ba rami, domin kada ya faɗa?
Masu iya magana na cewa, “idan ɓera na da sata, daddawa ma na da wari”. Wannan labari an ce ya fito ne daga datfarin kwafin rahoton da aka bankaɗo na “Accelerated Stabilization And Adɓancement Plan” (ASAP) da Ministan Kuɗi, Wale Edum, ya gabatar ga Shugaban Ƙasa Tinubu a makon da ya gabata.
Rahotan na ASAP da aka tsara kamar yadda daftarin ya nuna cewa, an shirya shi ne domin a tunkari dukkan manya-manyan ƙalubalen da ya ke damun ƙasar nan, wai kamar yadda rahotan ya nuna an yi ƙiyasi kuɗaɗen da ake kashewa kan tallafin man fetur a wannan shekarar ta 2024 ya kai Naira Tiriliyan 5.4, wanda ya zarce Naira Tiriliyan 1.8 da aka kashe a bara. Wannan ya yi nuni da cewa, idan har za a kashe waɗannan kuɗaɗe a tsahon wata shida, kafin ƙarshen shekara zai kai Naira Tiriliyan 10.8 kenan.
Tambayar a nan ita ce, waɗannan maƙuden kuɗaɗe da ake ba wa wasu ’yan lelen Najeriya da ba su wuce mutane 50 ba gaske ne? Ko kuma zuƙi ta malle ne?
Maganar gaskiya idan har labaran da kafafen yaɗa labarai da kafafen sada zumunta suke yaɗawa, zuƙi ta malle ce, ba gargaɗi ne kawai daga mutane irin su Minista Bayo Onanuga za ta fito ba, a’a, daga haƙun labarai, wato mutane irinsu Ministan Labarai da Wayar Da Kan Jama’a, Muhammad Idris, kuma duk wanda aka kama da yaɗa labarai na shifcin gizo ya ɗanɗana kuɗarsa, kada a fake da ’yancin fadar albarkacin bakin mutum. Idan har tsarin dimukraɗiya ake bi kamar a Amurka da kuma Yammacin Yurai.
Tambaya haka ake yi a ƙasar uwar gijiyar damakaraɗiya? Amsa ba haka su ke yi ba, ba haka kawai, domin ka na kafar yaɗa labarai, ka riƙa faɗar son ranka ba tare da ka je ka sami cikakken bayani daga asalin wanda labari ya fito a huruminsa. Hatta a ƙasashen da suke da’awar jagororin dimukraɗiyya batun ‘rumour’ (jita-jita) haramun ne. Duk wanda aka kama da yaɗa jita-jita zai ɗanɗana kuɗarsa, wato sai an gasa masa aya a tafin hannunsa, saboda gobe kada ya sake.
A dukkan addinai a wannan sarari na subuhana, musamman addinin Musulunci yaɗa jita-jita haramun ne yana kai matsayin ridda, wato fita daga cikin addinin, sai addu’ar Allah ya kiyashe mu.
Mu guji yaɗa jita-jita domin kuwa jita-jita fitina ce a kwance ta na zubar da mutuncin mai yaɗa ta, kuma babu wata magana da mutum zai yi nan gaba a saurare shi, domin ya zama ‘maƙaryaci’.
Haka ta sa yara suke cewa, “ƙarya zagin Allah”, saboda nauyin ƙarya, mutanen kirki ba sa mu’amala da maƙaryaci. Mu guji yaɗa jita-jita, koda kuwa kana da yaƙini a kan maganar.
Shawara ga hukumomi kada su riƙa ɓoye labarin ƙasa a kowanne fanni walau a fannin tattalin arziki siyasa, zamantakewa har ma a fannin tsaro, wannan ta sa ’yan ta’adda irinsu Bello Turji za su riƙa ƙaryata hakumomi a bainar jama’a. Wannan ƙaryatawa yana ba wa ƙasurguman ’yan ta’ada wani matsayi a idon ’yan ƙasa. Haka kuwa ta na faruwa ne saboda rashin tantance labari.
Kafofin yaɗa labarai kamata ya yi, ko kuma wajibi ne a gare su suna da dukkan hotunan ‘news makers’, mutanen kirki da na banza komai yawansu tare da ‘brief biography’, wato taƙaitaccen tarihinsu.
Saboda haka za a guje wa wannan ɓarna da ake tafkawa. Kuma zai rage ganin shugabanni a matsayin maƙaryata. Haka masu labarai su fahimci matsayin ‘goɓernment policy statement’; wato da’awa ko buri ko manufa ko hange da kuma aniya wajen bayar da labarai.
Duk wani daftari na gwamnati da ya faɗo hannun masu bayar da labarai sai sun tauna, taunawa kuma ta fahimta, wacce irin rariya za ka yi amfani da wannan labari? Ko kasuwa ka je za ka sayi rariya za a shaida ma ka cewa, rariya daban-daban har dozin guda su ke da ita kuma kowacce da irin garin da ta ke fitarwa tun daga zaga-zaga har mai gari tilus, kamar kuncin jariri kafin ranar sunansa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, wannan ƙalubale ne a gare ka, musamman kwamatin da ka kafa da su zo da dabarun yadda za a cusa kishin ƙasa a zukatan ’yan ƙasa, rage yaɗa labaran zuƙi ta malle a kafofin yaɗa labarai da na sada zumunta shi kansa kishin ƙasa ne, don haka sai a yi hattara.
