Har yanzu akwai masu kallon karatun mace a matsayin bariki – Asma’u Karofi

Spread the love

“Ina so in zama fitacciyar mai sharhin wasanni”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Gimbiyarmu ta wannan mako ba kowa ba ce sai illa, Asma’u Hamza Karofi, fitacciyar ‘yar jarida, mai sharhin wasannin ƙwallon ƙafa, kuma ɗaya daga cikin matan da ke gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ a tashar Arewa 24. Gimbiyar tamu wacce ƙwararriya ce wajen gabatar da shirye-shiryen talabijin da sharhi kan abubuwan da suka shafi cigaban matan Arewa, ta shaidawa wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu cewa burinta watarana ta kai kamar ƙwararriyar mai sharhin wasannin ƙwallon ƙafar turan nan Kate Abdo, ko ma ta zarce ta a fagen shahara. Ga yadda hirar tasu ta kasance. 

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki. 

ASMA’U KAROFI: Sunana Asma’u Hamza Karofi. Ina ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ a tashar Arewa 24. Ina kuma aikin tace hoton bidiyo, sannan ina taɓa kasuwanci. Yanzu haka kuma ina shirye-shiryen fara gabatar da wani shiri na podcast a manhajar YouTube, nan ba da daɗewa ba, in sha Allahu. Ni ce ‘ya ta shida a cikin ‘yan’uwana mu 13. Sannan Allah ya albarkace ni da yarinya ɗaya. Alhamdulillah! 

Ko za ki ba mu tarihin rayuwarki?

An haife ni ne a Jihar Kaduna, kuma na yi karatun firamare da sakandire duk a Kaduna. Sannan na yi aure ina ajin ƙarshe na sakandire wato (SS3), wannan ya sa ban samu cigaba da karatuna zuwa jami’a ba, sai a shekarar 2016. Na samu damar zuwa Jami’ar Bayero ta Kano inda na karanci ilimin aikin jarida da tattara bayanai.

Waɗanne abubuwa ne za ki iya tunawa da suka taimaka wajen gina rayuwarki yayin tasowarki?

To, a gaskiya abinda ya fi tasiri wajen gina rayuwata shi ne, iyalin da na fito. Yadda muka tashi kuma aka yi tarbiyyar mu an nuna mana muhimmancin riƙo da addini. Don haka mun rayu cikin kiyaye dokokin ubangiji da sanya Allah Maɗaukakin Sarki cikin duk wani abu da za mu yi. Saboda haka duk wani ƙalubale da ya zo mana a rayuwarmu, muna nuna tawakkalinmu da miƙa al’amarinmu ga Allah. Kusan dukkan mu mun tashi da wannan a cikin halayyar mu ta yau da gobe. Zan iya ce maka nima wannan ne ya yi tasiri a rayuwata. 

Shin kina kallon kanki a matsayin wata mace ta musamman? Kuma me ya sa?

Ba zan ce ni wata mace ce ta musamman ba. Amma ina iya ƙoƙarina in ga na yi rayuwa mai kyau, kuma halayyata ta nuna irin tarbiyyar da na taso da ita a gidan mu. Bayan na girma na shiga cikin jama’a ina mu’amala da mutane daban-daban na fahimci lallai rayuwar da muka taso da ita ta musamman ce, don ina ganin ɗabi’un mutane iri-iri.

Ba mu labarin gwagwarmayar da ki ka sha ta karatu, da abin da ki ka fi tunawa lokacin karatu a sakandire ko jami’a?

Karatuna na Sakandire ya tafi babu matsala. Na yi ƙaramar sakandire daga aji ɗaya zuwa uku Dembo International School, sai kuma na wuce babbar sakandire a Jinie Schools. Na so na karanta aikin jarida wato Mass Communication, amma ban samu wannan damar ba sai aka ba ni kwas ɗin nazarin aikin watsa labarai da tattara bayanai, wanda duk kusan abu ɗaya ne. Sai dai na ɗan fuskanci matsalar fahimtar ilimin sarrafa kwamfiyuta a lokacin, amma a hankali daga baya na fahimci yadda kwas ɗin yake. Ban fuskanci wani ƙalubale sosai a karatuna ba. Alhamdulillah. 

Shin kin fuskanci wani ƙalubale a gida ko bayan kin yi aure kan batun neman ilimi?

Ban fuskanci wani cikas ba gaskiya. Don gidan mu gidan ‘yan boko ne, na samu goyon baya sosai. Kuma na yi karatuna cikin kwanciyar hankali, kodayake na san wasu yaran mata ba sa samu irin gatan da na samu ba, saboda rashin fahimtar muhimmancin ilimin daga wajen iyayensu ko ƴan’uwa, da kuma rashin wadatar da za su cigaba da karatun.

Yaya ki ke kallon cigaban da ilimin ƴaƴa mata ke samu a Arewa?

Alhamdulillah, ana samun cigaba sosai a yanzu, ba kamar a shekarun baya ba. Kodayake ba yadda ake buƙata ba ne, har yanzu a wasu wuraren ba a bari yarinya ta cigaba da karatu ko da ta yi aure. Kuma ana ƙyamar matan da suka yi karatu mai zurfi. Har yanzu akwai masu kallon karatun mace a matsayin bariki ko buɗewar ido. Ko a riƙa yi mata ganin kamar ba ta da kunya ko makamancin haka. 

Me yake baki sha’awa a aikin jarida? Dama layin karatunki ne ko daga baya ki ka samu kanki a ciki?

Kamar yadda na faɗa a baya, dama can a jami’a karatun da na yi kenan. Tun ina ƙarama na taso da son in yi aikin jarida, kuma bayan na girma na fara gudanar da aikin, na fahimci yadda aikin yake. Kuma babu shakka aikin ya bani ikon shiga mutane da yawa, na ga al’adu daban-daban kuma na yi hulɗa da su sosai. Abin da ya fi birgeni shi ne, haɗuwata da mutane ya taɓa rayuwar wasu da dama ta yadda ban yi tsammani ba. 

Yaya ki ka samu kanki a shirin Mata A Yau na Arewa 24?

Arewa 24 daman na taɓa aiki da su a shekarar 2017 a matsayin edita, da na koma makaranta sai na ɗan ja da baya da aikin. Sai bayan da na samu natsuwa ne daga baya sai na haɗu da wata mata da ta fuskanci ina da baiwar fitowa a talabijin, a maimakon bayan fage, don haka sai ta fara sanya ni ina gabatar mata da shirye-shirye a wata tashar talabijin. Daga nan ne na koma tashar Trust TƁ inda na riƙa gabatar da shirin sharhin wasanni wato Sports Analysis. To, daga nan ne kuma arewa24 suka sake ɗauko ni.

Ta yaya ki ke ganin tasirin da shirin ke da shi wajen saita tunanin matan Arewa?

Shirin ‘Mata A Yau’ yana da tasiri sosai, musamman ta fannin ilimantar da mata. Shirin ya zama kamar wata ƙaramar makaranta dake samar wa mata damar samun ilimi da isa garesu a ko’ina suke, daga birane har da rugage da ƙauyuka. Kuma in za ka duba za ka ga duk darussan da muke tattaunawa a kai, sai mun kawo wani ƙwararre a fannin wanda zai ƙara fayyace wasu muhimman abubuwa sosai a game da abin da muke magana a kai. 

Gaya mana abin da ya ja hankalinki a harkar wasannin motsa jiki?

Gaskiya na fara kallon wasannin motsa jiki ne musamman ƙwallon ƙafa tun shekarar 2002 zuwa 2003. A lokacin ina yarinya ina tare da ‘yan’uwana maza waɗanda muka taso tare, waɗanda kuma harwayau masoya kallon wasannin ƙwallon ƙafa ne, zama da su ne suka sa min sha’awar kallon wasan ni ma. Kasan an ce zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai. Na girma ne da son abin, kuma gaskiya babu abin da ke min daɗin kallo kamar ƙwallon ƙafa. 

Ke ma kina taɓa ƙwallon ƙafar ne? 

(Dariya) A’a, ina dai kallo! 

Wacce gudunmawa mata za su iya bayarwa a wannan ɓangaren na wasanni?

Akwai abubuwa da dama da za a iya yi a janyo hankalin mata matasa da ke sha’awar harkokin wasanni, don in sun gani su ma su san za su iya. duk da kasancewar ba abu ne da aka saba gani ba a nan Arewa. Sannan kuma za su iya koyarwa wato coaching kenan da wayar da kai kan mata a harkokin wasanni, ba ƙwallon ƙafa kaɗai ba, har da sauran ɓangarorin wasannin motsa jiki, da nema musu goyon baya da tallafi daga hukumomi da masu hannu da shuni, don a kare muradun yara mata. Sai kuma batun yi musu jagoranci da nuna musu yadda ake sharhin wasanni ta kafafen watsa labarai, kamar tashar CBS da ke nuna wasannin Champions League, shugabar su mace ce, Kate Abdo, kuma tana aiki da ƙwararrun ƴan wasa da suka yi fice a wasannin ƙwallon ƙafa a baya irinsu Thierry Henry, da Jamie Carragher, amma ita ke jan ragamar shirin. 

Yaya ki ke kallon ƙalubalen da addini ko al’ada ke haifarwa wajen daƙile sha’awar mata a fagen wasanni?

Haka ne. Ka san wani lokaci ana cakuɗa addini ne da al’ada, har ma wani lokaci ka kasa iya tantance wane ne a ciki. Wasu lokutan shi ya sa muke da malamai da za su iya mana fatawa ko su fayyace mana hukunce-hukuncen addini a yadda Musulunci ya koyar. Don haka ina ganin matuƙar abu ba haramun ba ne to, yarinya ta je ta yi kawai, Allah Ya bata sa’a. 

Shin kina tunanin kai wa wani babban mataki a fagen sharhin wasanni da ki ke yi? 

Ka ji misalin da na bayar na Kate Abdo ai, to in sha Allah za mu kai can, mu wuce ma bi’iznillah. 

Banda aikin jarida da fagen wasanni, wanne abu ne tun tasowarki ki ke sha’awar yin sa a rayuwarki, amma ba ki samu dama ba?

Aikin jarida ai ba a sharhin wasanni kaɗai na tsaya ba, ina matuƙar son kyautata wa yara mata da kuma sanar da su abubuwa da yawa musamman yadda za su fahimci damarmakin da suke da su a rayuwarsu. Mafi yawancinmu muna tunanin bamu da zaɓi a rayuwarmu a lokacin da muke ganin ba za mu samu mai goyon bayanmu a abin da muke so ba. Shi ya sa nake so na ɓullo da sabon shirin podcast da nake so in fara, wanda zai riƙa duba gudunmawar mata a harkokin rayuwa daban-daban. Yadda za mu riƙa wayar da kai matasan mata yadda za su inganta rayuwarsu. 

Yaya ki ke ji a ranki irin tsangwamar da aka riƙa nunawa shirin ‘Mata A Yau’ da masu gabatar da shirin a baya?

Ba laifin su ba ne, su ma rashin sani ne. 

Idan sun natsu za su gane mu ba maƙiyansu ba ne, amma abokan tafiya ne. Muna ƙoƙarin sanar da mata ne yadda za su zama abokan tafiya na ƙwarai a cikin al’umma.

Mene ne shawarar ki ga masu kallon shirin mata da maza?

Su saki ransu, su fahimci mu da buɗaɗɗiyar zuciya. Sannan mata mu kula da junan mu, ba dole ne sai mun yi gasa da wani ba, kowa da rabonsa ya zo duniya! 

Wanne abu ne ki ka fi jin daɗin yi a lokacin da ba kya komai a gida?

Kallo! Ina son kallo sosai, gaskiya!!

Shin kina da wata sana’a ko kasuwanci da ki ke yi a gida?

E, a baya dai ban yi tunanin yin wata sana’a ba. Amma bayan tattaunawa da wasu ƴan’uwana ni ma na fara tunanin kafa wani kasuwanci da zan riƙa yi daga gefe, ina samun wasu ƙarin hanyoyin samun kuɗi.

Wanne abu ne ki ka fi son a miki kyautarsa, a matsayin gift?

An min tarbiyyar kada na riƙa sa rai da wani zai yi min wani abu. Don haka tunanin ko me nake sa rai a min kyautarsa ba ya zuwa raina. Komai aka yi min kyautarsa ina nuna jin daɗi sosai. Sai dai nakan ji farinciki sosai, idan aka yi min kyautat doguwar riga, don ina sonta sosai (Dariya). 

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Ina yawan tuna wata karin magana da ake ce wa, ‘Daɗina da gobe saurin zuwa’. Amma kuma ni a falsafar rayuwata, abin da kullum nake gaya wa kaina shi ne, 

“Duk abinda ba dole ba, a barshi.”

Na gode.

Masha Allah. Ni ce da godiya.

By ukarofi