’Yan sandan Indiya sun cafke matashin ɗan Nijeriya kan zargin damfarar ’yan mata

Spread the love

’Yan sandan birnin Delhi sun kama wani ɗan Nijeriya mai shekara 29 da ake zargin ya yaudari mata fiye da 100, ya karɓi kuɗaɗe daga hannunsu a Indiya.

‘Yan sandan sun ce ya yi amfani da sunan wani ɗan kasuwa ɗan asalin Koriya mazaunin Birtaniya a wata manhajar ta soyayya da kulla aure.

A cewar jaridar Hindustan Times, wanda ake zargin sunansa Stephane amma yana amfani da sunaye na ƙarya “Dominic” da “Duck Young,” an kama shi a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun cafke matashin ɗan Nijeriyan a wani ɗakin haya da yake zaune a Tilak Nagar, da ke yammacin birnin Delhi.

Mahukunta sun ce wanda ake zargin ya yi amfani da tsarin damfarar soyayya, inda su ke amfani da shafukan sada zumunta da na soyayya don ruɗar da mata.

’Yan sanda sun gano cewa, abokan aikin da ɗan Nijeriya ya haɗa baki da su, sun riƙa kiran matan da sunan cewa su jami’an gwamnati ne.

Rahoton bincike ya nuna cewa sun riƙa neman kuɗi daga hannun matan da sunan za su wanke Stephane daga wani zargi na ƙarya.

‘Yan matan sun riƙa tura kuɗin da aka nema da tunanin su na taimakon saurayinsu ko ma wanda za su aura bayan ƙulla soyayya a kafar sada zumunta.

Asirin ‘yan damfarar ya fito fili ne bayan wata mace mai suna Anjali ta kai rahoton damfarar da aka mata na rufi 48,500.

Ta bayyana cewa, “Duck Young” ya yi iƙirarin cewa an tsare shi a filin jirgin saman Mumbai, daga baya ta samu kiran wasu mutanen da suka yi iƙirarin jami’an hukumar shige da fice ne, suka nemi ƙarin lakh biyu.

‘Yan sandan sun gano cewa Stephane ta hanyar bin diddikin kira, asusun banki da kuma ayyukansa a kafafen sada zumunta.

Lokacin da aka kama shi, an samu waya cike da bayanan ƙarya da hirarraki da mata fiye da 100.

Subun ɗan Nijeriya ta cika a India.

A yayin bincike, ya amsa cewa ya shiga Indiya tun 2019 da bizar yawon buɗe ido na watanni shida kuma ya yi amfanni da fasfon Cote d’Iɓoire domin guje wa takunkumin da aka sanya kan ’yan Nijeriya a wancan lokaci.

Bayan bizar ta ƙare kuma kuɗinsa suka ƙare, sai ya farar harkar yaudarar ‘yan mata ta yanar gizo.

By ukarofi