Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ
Wato ni kam na dade da daina mamakin duk wani son rai da Malaman Izala zasu nuna saboda hujjoji na kamar haka:
Na farko dai, wanda ya zamar min cikamakin hujja da ke nuna cewa kare kungiya, siyasa ko wani son rai shi su ka sa a gaba fiye da komai, shine a lokacin dambarwa Gandollar, Malaman Izala sun yi gungu su ka kai caffa ta goyon bayan ga Ganduje. To ba a nan munin abin ya tsaya ba, a’a, a bayanin shugabansu, Sheikh Sale Pakistan wanda aka watsa a rediyo ya furta cewa “Yadda Allah ya wanke Aisha daga zargin Zina, haka muke sa ran Allah zai wanke ka daga wannan zargi (na cusa dollar a babbar Riga)” wannan lamari shine gaya a wuri na na nuna son zuciya.
Sannan idan muka sake waiwaye a lokacin mulkin Jonathan da Boko Haram ta addabi Arewa, Malaman Izala sun yi caa a kan Jonathan, amma su ka yi tsit a kan maharan Boko Haram. A karshe sun mayar da zaben 2015 tamkar jihadi yadda sai da aka kayar da Jonathan. Amma a lokacin Buhari, saboda ya ja su a jiki, duk da mummunar illar da Buhari yayi wa Arewa da Musulmi, ba ruwansu, sai ma fatawoyin haramta zagin shugaba ko yi masa bore ko zanga-zanga.
Kamar yadda na sha fada a baya, illar Malaman Izala a wajena da mafiya yawan mutane shine watsi da su ka yi da ginshikin wa’azi da Allah ya wajabta mana cikin; ƙ16:125 “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.”
Amma sanin kowa ne babu wata kungiyar addini a musulunci da ta yi watsi da wannan ginshikin irin Yan Izala. Domin tun asali sai su ka kirkiri Kalmar “Takfir” wato kafirta duk wani wanda ya saba da ra’ayinsu.
Haka Kuma Allah ya tabbatar mana da cewa babu wata al’umma a wani zamani da za ta kewaye Ilimi a ma’anar ayar; ƙ31:27 “Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba. Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.”
To, amma ita ma wannan aya sun yi watsi da ita a aikace ta hanyar nuna cewa Ilimin addini ya kare daga Salaf, duk wani abu da ya saba da su ba daidai ba ne. Wannan dalili ya sa wasu ma ke ikirari cewa an kulle kofar ijtihadi gaba daya. Dalilin haka ya sa sakamakon Malaman Salaf irinsu Ibn Hanbal, Ibn Taimiyya Ghazali dss sun tsayar da ci gaban musulmi ta fannonin kimiyya da falsafa, ta yadda har wasu ke daukar wadannan ilimai sun saba da musulunci ko ma Kafirci ne. Kamar yadda na bada misali kwanan nan da dambarwata da marigayi Sheikh Jafar a kan husufi, inda kuma hujjoji na suka bayyanar da jahilcinsa a wannan bangare, duk da cewa ni ban kama ko kafarsa a Tafsir da ilimin hadisi ba.
Kowa ya ga yadda Malaman na Izala su ka yi caa a kan Abduljabbar, har sai da su ka ganshi a kurkuku sakamakon katobararsa wajen yin amfani da kalmomi da basu dace a ce ko kan mahaifinsa Nasiru Kabara ya jingina su ba, ballantana Manzon Allah, duk da cewa ya na kokarin kore hadisan ne ba jaddada su ba. Amma Allah hakimun, sai ga shi yau an wayi gari, kwabo-da-kwabo yadda Abduljabbar ya yi waccan katobara sai ga Lawal Triump ya yi, amma sun tada jijiyoyin wuya su na kare shi.
Kada mu manta cewa, Allah ne da kansa ya ce mana cikin ƙurani; ƙ49:2 “Ya ku wadanda su kayi imani, kada ku daga saututtukan ku bisa sautin annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a Magana, kamar bayyanawar sashen ku zuwa sashe, domin kada ayyukanku su baci, alhali kuwa baku sani ba.”
Babu wata aya, a fahimta ta, wadda ta fitar da irin girman da annabi yake da shi a wurin Allah kamar wannan. Dalili kuwa shi ne, babu wani mahaluki da Allah ya ce idan aka saba masa (ba a kan wani hakki na shari’ar Allah ba) a’a saboda martabarsa, za’a iya karo da bacin ayyuka.
Abubuwa biyu kawai a musulunci ke bata aiki, wato na farko yin shirka ko kuma aiki na riya. Wannan aya kawai, ta isa ta nuna mana girman annabi a wajen Allah da a wajenmu. To Yaya wani zai jingina wasu misalai na nakasu da Manzo?
Don haka duk abinda aka zargi Abduljabbar, ya hau kan Lawan Triump, Kuma na yi Imanin dukkansu korewa su ke kokarin yi ba jaddadawa ba, amma saboda bangaranci, a wajen Izala Abduljabbar ya cancanci hukunci, amma Lawal Triump ba shi da laifi.
Wannan halayya ta Malaman Izala ta sake karo Kai tsaye da wani ginshikin koyarwar Ubangiji a cikin Suratul Nisa’i; ƙ4:135 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.”
A ƙarshe, ina kira gare mu baki daya, matukar mu na son zama lafiya da samun nasara da hadin kai, dolen dole mu rika aiki da wannan aya, ita kadai za ta yi mana maganin son rai da rashin adalci. Mu zama daya a gaban Shari’a, wato ko wanene ya yi ba daidai ba mu bada shaidar haka, ko iyayenmu ne ko mafi kusanci a rayuwa ta kowacce fuska kamar yadda wannan aya ta yi mana gargadi. Sannan malamai su kaucewa amfani da karfin mulki domin tabbatar da wata bukata tasu. Domin a wannan dambarwa kawai, akwai babban darasi tunda a baya APC, Ganduje da Malaman Izala sun hade kai, to yau Kuma idan NNPP, Abba da wadanda ba yan Izala ba su ma sun hade kai? To wa ya san kuma gobe, wa Allah zai baiwa mulki? Jama’a a yi hattara!!!
Malam Ali manazarci ne a Kano
