‘Yan sandan Kanada sun kama ƴar Nijeriyar da ta yi barazanar saka wa Yarabawa guba

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƴan sanda a jihar Toronto da ke ƙasar Kanada sun kama wata ƴar Nijeriya mai suna Amaka Sonnberger da ke zaune a ƙasar wacce ta yi barazanar sanya guba wa al’ummar Yarbawa da Benin.

An kama matar ne mai shekaru 46 a ranar Lahadi bayan bincike da aka gudanar kan saƙon da ta yaɗa a yanar gizo a ranar 25 ga watan Agusta wanda ke ɗauke da barazana ga wasu keɓaɓɓun mutane a Nijeriya.

Ƴan sandan sun gabatar da matar ne a kotu a ranar 2 ga watan Satumba inda ake tuhumar ta da laifin furta kalamai da ke kunshe da barazana.

Sonnberger ta ce za ta fara sanya guba acikin abinci da abin sha na ƴan Nijeriya yayin da ta je wajen aikinta.

A kwanakin baya ne Majalisar wakilai da hukumar kula da ƴan Nijeriyar da ke waje suka buƙaci hukumomi a Kanada su gudanar da bincike akan matar.

By Babaji