Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Aƙalla mutane 10 ne ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yiwa garin ƙawanya da misalin ƙarfe 2:00 na daren jiya.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun ɗauki sa’o’i da dama suna gudanar da ayyukan su a garin.
“Ina so in sanar da kai cewa ‘yan bindiga sun kai hari a garin mu Maru a daren jiya da misalin ƙarfe 2:00 na dare, abin baƙin ciki ne, an yi garkuwa da surukina wanda ke riƙe da muƙamin babban limamin babban masallacin Maru, Alhaji Salisu Suleman tare da matansa biyu da ‘ya’yansa bakwai”. Ya ƙara da cewa
A cewarsa, a yayin harin, ‘yan ta’addan sun fara gudanar da ayyukan su gida-gida tare da kwashe dabbobi, kayayyaki masu daraja na miliyoyin Naira mallakar al’ummar garin.
Ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Jihar Zamfara da su kawo musu ɗauki ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro domin kare al’umma daga hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai masu a ko da yaushe.
“Ina kira ga hukumomin ƙasar nan, da su ƙara tura jami’an tsaro a garin mu domin kare rayukan mu daga waɗannan ‘yan ta’adda”. Yace
Wakilinmu ya tattaro cewa al’ummar Maru sun toshe babbar hanyar dake zuwa Sokoto dangane da lamarin a yau Alhamis don nuna damuwarsu kan lamarin.
Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara ya shafe sama da watanni uku yana fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’addan, an yi garkuwa da mutane sama da 60 waɗanda da dama daga cikinsu har yanzu suna hannun ‘Yan’ta’addan.
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Asp Yazid Abubakar da wakilinmu yayi yaci tura, domin ba a kai ga samun dukkan layukan nasa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.