‘
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Mambobin ƙungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adanai da harkar noma ta Jihar Zamfara (ZACCIMA), sun taya shugaban su na jihar, Dakta Hassan Buhari murnar cika shekaru 62 da haihuwa.
Saƙon taya murnan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Disamba, 2024 ta hannun mataimakinsa Abubakar Chika Galadima wanda aka rabawa manema labarai a Gusau a yau Litinin.
Sun bayyana kyakkyawan shugabancin shugaban a matsayin shaida na gagaruman nasarori da kuma jajircewar sa na ciyar da tattalin arzikin Jihar Zamfara a gaba.
“A matsayinka na mai girma shugaban ƙungiyar mu ta Chamber of Commerce, bisa jagoranci na hangen nesa da sadaukarwarka sun bunƙasa tattakin arzikin mu da ‘yan kasuwa, tare da bunƙasa ci gaba da sabbin dubaru a sassa daban-daban na tattalin arzikin jihar mu ta Zamfara”.
“Tasirin ka ga ƙungiyarmu da sauran al’umma yana da matuƙar kima, kuma muna alfahari da kasancewa tare da kai a kan manufofin ka na samar da ci gaba da bunƙasar fannin tattalin arziki a jihar Zamfara”.
Hakazalika, ‘yan ƙungiyar sun yi alƙawarin bayar da dukkan goyon baya da haɗin kai ga shugabancin Dakta Hassan Buhari a matsayin shugaban ZACCIMA na jihar ta Zamfara domin ci gaban jihar ta fuskar tattalin arziki.