Yanzu matan Kannywood za su iya harkar fim ba tare da an ga fuskarsu ba – Halima Ben Umar

Daga AISHA ASAS

Labarin yunƙurin da mata ke yi, don kafa tarihi a masana’antar finafinai ta Kannywood ta hanyar shirya fim ɗin da mata zalla suka yi aikinsa, tuni ya karaɗe kunnuwan dubunnan al’ummar Hausa, kai ma har da wasu ɓangarori na wannan qasa tamu mai albarka. Da yawa sun tofa albarkacin bakinsu da bayyana ra’ayinsu. Wasu na ganin abin a matsayin cigaba, yayin da wasu ke ganin sa a matsayin hurimin da su matan bai kamata su shiga ba, sannan wasu kuma na  ganin abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Da wannan ne shafin Nishaɗi na wannan mako ya tattauna da shugabar wannan tafiya ta shirya fim ɗin mata zalla, wanda wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba (NGO), Girls’ Nation, ta ɗauki nauyi, Hajiya Halima Ben Umar, don amsa tambayoyinku kan wannan gagarumin yunquri da kuma samun sahihancin wannan horo da mata zalla suka samu a masana’antar Kannywood. A sha karatu lafiya:

BLUEPRINT MANHAJA: Ki na ɗaya daga cikin matan da suka ɗaura haramar kafa wani tarihi a masana’antar finafinai ta Hausa, wato Kannywwod, inda aka ce za a shirya fim irinsa na farko da mata zalla za su yi aikinsa, wato dai tun daga masu aikin kamara, sauti, tacewa da sauransu. A matsayin ki ta mai shirya wa, za mu so mu ji yadda wannan yunƙurin ya yiwu da kuma manufar yin sa.

HAJIYA HALIMA: Alhamdu lillah. Da farko dai akwai Baharu, shi ya zo ya min magana, ya ce, akwai wata ƙungiya, suna so za su yi wa mata bita kan yadda ake yin harkar fim. Ya ce, ya san Ina da sha’awar finafinan Kannywwod. Wannan haka ne, domin na yarda Kannywwod sana’a ce, kuma a kullum Ina faɗar kura-kuranta don a samu a inganta harkar.

A nan ya sanar da ni buƙatar ƙungiyar, wato a samar mata ƙungiyoyin mata, waɗanda za a iya tafiyar da su. Ya nemi in shige gaba kasancewar Ina da ɗan sani kan harkar fim da kuma na ƙungiyoyi. To, shi ne na amince, bisa sharaɗin sai na ga manufofin ita ƙungiyar kan wannan aiki. Sai na karanta tsari da buƙatarsu. Idan ya yi daidai da addinina da al’adata zan yi. 

To bayan karantawa, gaskiya na gamsu, kuma na fahimci hanya ce da za ta ba wa mata dama da yawa, ta inda ba dole sai ta fito a fim ba, zata iya yin harkar fim ba tare da an ga fuskarta ba ma. To sai dai a tawa niyyar ba zan shiga ciki ba, na dai bada ‘yan ƙungiyarmu biyar, sai dai a zaman da aka yi ne, na fahimci abin na da matuƙar muhimmanci, don haka a kwanakin biyar na farko duk da ni aka yi, Ina sauraro, kuma na kan yi ‘yan tambayoyi.

Hajiya Halima Ben Umar (a tsakiya)tare da mata zalla da suka ɗauki horonshirin fim da ƙungiyar Girls’ Nationsuka ɗauki nauyi a Kano kwanakinbaya

Kuma idan yaran sun yi ba daidai ba, zan tashi in yi faɗa. To fa a nan ne suka ce wai ni ce ‘producer’. Na ce ni da shekaru haka da na kusa rufe sittin, ina zan iya.

To fa nan dai aka ta roqona, kowa ya sa baki. To fa a nan shigata ciki ya samo asali. Tun a nan muka fara maganar ‘script’. To fa nan aka dinga yi, a je a dawo kin san sha’ani da mata. Shi kansa ‘script’ ɗin kafin a yi matsaya kansa ba ƙamar wahala aka sha ba.

Duk da cewa shi wannan fim ɗin ba irin na Kannywwod ba ne, fim ne gajere na minti 25. Wanda ke nuni da irin ƙalubalai da mata ke fuskanta da kuma gwagwarmayar rayuwa da suke yi. Daga ƙarshe kuma ya samar da mafita. 

Wato a wannan aiki ne na jinjina wa masu yin fim, domin a lokacin da muke kallon fim sai muga kamar ba wani aiki ba ne, ashe jan aiki ne. Na fahimci hakan a wannan aiki da muka fara. 

Ko kun fuskanci ƙalubale a wannan tafiya?

Alhamdulillah, mun yi kwana huɗu mu na yi, kuma gaskiya mun samu ƙalubalai da yawa da ba mu yi tunanin za mu same su ba. Duk da dama komai na rayuwa tare yake da ƙalubale. Da farko dai mun samu matsalar sarewar gwiwa, domin wasu daga cikin mu da aka fara da su da yawa sun gudu.

Kinga wannan babban ƙalubale ne. Ana tare da yawa, ana aiki, sai a yi ta ficewa, tunda wasu suna ganin ba wani kuɗi da yake shigowa, yayin da wasu na ficewa ne saboda suna ganin akwai kura-kuran da ake samu. Da sauransu.

Sai dai gaskiya mun yi tsari mai kyau da ko Kannywwod ɗin ba kowa ne ke yin wannan tsari ba. Kamar misali, kafin a fara ‘rehearsal’, mun yi table reading’, wato za a haɗu duk waɗanda za su fito a fim ɗin, su ga juna, kuma kowa ya karanta nasa ‘lines’ a zaune, kuma ka karanta a tsaye, kafin a kai ga yi tare.

Sannan ta ɓangaren kamara da muka yi amfani da ita, bana jin ko Nollywood suna da irin ta.

Shin duk wanda yake cikin wannan bita an koya masa amfani da kyamarar?

Kowa kuwa an koya masa. Ko ni nan na koya. A wannan aikin ma ni na yi kamara. Dama idan ka yi kamara a nan, sai gaba ka tafi ‘sound’ ko haske, haka dai aka ta juyawa, kowa ya yi. Idan ka yi wannan yau, gobe sai ka yi wani abin daban.

To ya kika ga ƙwazon yaran, kasancewar yara ne masu ƙarancin shekaru?

Gaskiya ban taɓa ganin yaran da suka burge ni ta ɓangaren ƙwazo irin su. Kinga na ɗaya, ba su tava aiki da kamara ko haske, ko sauti da sauran ababen da ake amfani da su, amma kowannen su na tare da ƙwarin gwiwa, kowacce na sha’awar yi, kuma suna kutsawa dukka ɓangarorin.

Sun sa jajircewa a gaba, wanda hakan ya sa ake yin aikin ba fushi cikin farin ciki. Kuma su ma waɗanda suka koyar gaskiya sun yi namijin ƙoƙari, domin shi sha’ani na koyarwa akwai wahala. Sun yi iya yi har kowa ya fahimci abinda ake so a gane.

Kuma akwai wani salo na koyarwa da suka yi da ya birge ni. Za ki ga idan a karatun aka yi tambaya, idan wani ya bada amsa, sai kiga an masa kyautar ‘t-shirt’ ko dubu ɗaya ko biyu. Sai ki ga kowa na sha’awar a ce shi ne ya bada amsar.

Gaskiya ba abinda za mu ce sai godiya ga Allah, domin duk da matsalolin da muka dinga cin karo da su, tun daga na ‘location’ da sauransu, mun samu nasarori da dama har Allah ya kawo aka kammala.

Wane tasiri ki ke ji wannan fim zai yi?

Tasiri na farko dai shi ne, bitar da aka yi wa yaran da kuma yadda ta yi tasiri a rayuwarsu. Domin bai fi mutum ɗaya ko biyu ne kawai muka ɗauka daga waje ba, amma duk masu aikin da kuma da yawa na jaruman sun fito ne daga cikin waɗanda aka ba wa wannan horon. Kaga an samu cigaba tun a nan. Domin da yawa ko da suka zo, ko magana ba sa iya yi a cikin mutane.

H-D; Hajiya Halima Ben Umar, tsohonSakataren MOPPAN na Kano, SalisuOfficer, tare da Editan BlueprintManhaja, Nasir S. Gwangwazo, a wajentaron bayar da horon fim ga mata zallaa Kannywood

Kenan wannan horon da aka yi ya wayar da kan yara, ya ba su sabuwar rayuwa?

Ƙwarai da gaske. Don akwai wata daga cikin mu da ta je koyon kamara kafin a fara wannan aikin. To bayan an gama ta je wani aiki a Kannywood, sai ta ke masu gyara cewar ba haka ake yi ba.

Shine suka ce wance (ita ma tana cikin waɗanda aka ba wa horon) ita ma ta zo tana mana wani sabon feleƙe. Ma’ana dai an zo masu da sabon abu. Ka ga a nan ma sai dai mu ce alhamdu lillah, tun a nan muna canji.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *