Eavans zai shafe shekaru 21 a gidan yari

Daga BASHIR ISAH

Yaznu dai ya tabbata cewa, ƙasurgumin mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudumeme Onwuamadike da ake yi wa laƙabi da Evans, zai shafe shekaru 21 a kurkuku bayan da kotu ta kama shi da laifin yin garkuwa da wani mai suna Sylvanus Hafia.

Evans zai yi zaman kason ne tare da wani abokin cin mushensa Victor Aduba.

A ranar Litinin Kotun Laifuka na Musamman mai zamanta a Ikeja, Jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo ta yanke wa waɗanda lamarin ya shafa hukuncin bayan da ta same su da laifin haɗin baki da yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia.

Laifin da kotun ta ce an aikata a ranar 23 ga Yunin 2014 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a Hanyar Kara, Amuwo Odofin a Legas.

An zarge su da yin garkuwa da Hafia tare da neman fansar Dala miliyan biyu.

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta tuhumar da aka yi musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *