
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa a matsayin sabon Babban Ministan Tsaron Nijeriya bayan shafe sa’o’i biyar a gaban ƴaƴanta a yau Laraba.
Da fari, Sanata Sani Musa (Neja ta Gabas) ya roƙi majalisar da ta ƙyale Janar Musa ya yi gaisuwar ban girma sannan ya tafi bayan sun masa wasu ƴan tambayoyi.
Saidai, wannan magiyar bata samu wuri ba domin kuwa waɗanda suka ƙi amincewa sun ce wajibi ne duk wanda aka bada sunansa a muƙamin minista, sai ya amsa karin wasu tambayoyi, lamarin da ya yi sanadin ɗaukar tsawon lokacin.
Daga bisani majalisar ta sake ɗaukar ɗumi a lokacin da wasu sanatocin suka nemi a tsayar da shi don ba’a kammala aiki akansa ba.
Bayan haka ne sai majalisar ta yi kira a gare shi da ya binciki dalilan da suak sanya sojoji suka janye daga makarantar Kebbi ana gab da garkuwa da ɗalibai.
Da yake jawabi, Janar Musa ya koka game da yadda harkar tsaron ke taɓarɓarewa a ƙasar, yana mai bayyana a matsayin abin takaici ga al’ummar Nijeriya.
Ya bayyana cewa, akwai buƙatar a samar da tsarin tsaro na musamman ga makarantu ganin yadda da dama daga cikinsu an bar su sake ta yadda suke da sauƙin kai farmaki.
Janar Musa ya ƙara da cewa, yana da muhimmanci a samar da matakan tsaro a garuruwa da suka haɗa da amfani da fasaha, damawa da al’umma da haɗin-gwiwar atisayen hukumomin tsaro.
