
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sanar da wasu sauye-sauye ga tsarin cirar kuɗaɗe a bankuna, inda ya soke tsarin iyakance adadin waɗanda za a zuba da faɗaɗa adadin cirar kuɗi a kowane mako zuwa N500,000 daga N100,000 da ake bi a baya.
An samu wannan jawabi ne a saƙon umarni da Daraktar tsare-tsaren kuɗaɗe da gudanarwa ta CBN, Dakta Rita Sike ta aike wa cibiyoyin kuɗi a Nijeriya, inda aka yi wa takardar taken ‘Rivised Cash-Related Policies’.
Ta bayyana cewa, CBN ya ɗauki matakin ne domin rage tsadar gudanar da tsabar kuɗi, daƙile barazanar tsaron kuɗaɗe da toshe ƙofofin satar kuɗaɗen kwastomomi da ake danganta wa tsarin tattalin kuɗaɗen Nijeriya.
Haka kuma, bankin ya ce duk da cewa tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta yanar gizo an samar da su ne domin ba wa ƴan Nijeriya wani zaɓi, nazari da yin kwaskwarima a kai suna da muhimmanci musamman bisa la’akari da yanayin tattali.
A ranar 1 ga watan Junairun 2026 ne tsarin zai fara aiki. An rushe tsarin iyakance zuba kuɗin ajiya na ‘fixed’, sannan an soke ƙarin cajis da ake yi sakamakon wuce iyakar adadin kuɗaɗe da ake zubawa a baya.
Sannan, CBN ya kuma sanar da cewa ɗaiɗaikun kwastomomi za su iya cire jimillar N500,000 a sati, yayin da masu asusun haɗaka kuma za a ba su damar cirar miliyan N5 a kowane wajen cire kuɗi. Hakan na nufin duk kuɗin ake son cirewa a lokacin sama da wannan, to za a caji ƙarin wasu kuɗaɗe a dalilin hakan.
Kazalika, an rushe tsari na musamman da aka fitar a baya da ya ba kwastomomi damar cirar miliyan N5 da na haɗaka kuma N10m.
A cewar CBN, kwastomomin da ke amfani da katin ATM, za su cigaba da samun damar cirar N100,000 a kullum, da jimillar N500,000 a mako, wato na waɗanda aka cire a na’urorin ATM, POS ko makamantansu.
Har’ilayau, babban bankin ya bayyana cewa dukkan kuɗin da za a cire sama da yadda ya ƙayyade, to hakan zai sa a samu karin cajis na kaso uku ga masu ɗaiɗaikun asusu ko kaso biyar ga masu na haɗaka, inda a saboda haka CBN zai dauki kaso 40, shi kuma bankin da aka yi hada-hadar da shi sai ya samu kaso 60.
Don haka ne CBN ya gargaɗi bankuna cewa su tabbatar da maƙare na’urorin ATMs da wadatattun kuɗaɗen domin buƙatar kwastomomi.
