
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Laraba ne Majalisar Dattawa za ta tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron (CDS), wato Janar Christopher Musa Gwabin domin tabbatar da naɗinsa a matsayin ministan tsaro, bayan Shugaba Tinubu ya bada sunansa a jiya Talata.
Shugaban mafiya rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya sanar da haka a wata takarda, inda ya bayyana matakin a matsayin abinda za a yi da nufin inganta harkokin tsaro da kariya ga rashin ɗorewa al’amuran ƙasa.
An bada sunan Janar Musa ne ƙasa kwana ɗaya da tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus.
Rahotanni sun tabbatar da cewa manyan kwamitocin majalisar sun kammala shirin gudanar da zaman tantancewar, inda ake sa ran Janar Musa zai yi bayani kan shirin da ya tanada don inganta tsaro, yaƙi da ta’addanci da kuma sake fasalin tsarin hulɗar jami’an tsaro da al’umma.
Janar Musa, wanda zai cika shekaru 59 a ranar 25 ga watan Disambar nan, ya riƙe muƙamin CDS daga shekarar 2023 zuwa watan Oktoban 2025.
Ya kuma taɓa samun kyautar gwarzon soja na Colin Powell a shekarar 2012.
An haifi Janar Musa a shekarar 1967 a Sakkwato, inda a nan ya yi makarantun firamare da sakandare kana daga bisani ya ka Kwalejin Ƙara karatu ta Zariya.
Ya kammala a 1986 sannan ya samu shiga makarantar sojoji ta Nigeria Defence Academy a shekarar, inda ya samu digirin farko a 1991.
