Zulaihat Dikko Raɗɗa ta jagoranci tattakin yaƙi da cin zarafin ’ya’ya mata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Raɗɗa, ta shiga sahun masu fafutukar yaƙi da cin zarafin ’ya’ya mata, yayin da ta halarci tattakin shekara–shekara na wayar da kan jama’a kan matsalolin fyaɗe, da sauran nau’ikan cin zarafi da mata ke fuskanta.

Hajiya zulaihat ta sami wakilcin uwar gidan shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Hajiya Maijidda Abdulkadir Mamman Nasir.

Tattakin, wanda ake gudanarwa kowace shekara daga 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba, ya tara ƙungiyoyi da dama masu fafutuka a faɗin jihar domin mayar da hankali kan wannan batu mai muhimmanci ga tsaron rayuwar mata da ƙananan yara.

A wannan karon, taron ya samu halartar ƙwararru da dama, ciki har da Dr. Jummai Garba, kwararriya daga TETRA TECH/Spring Project wadda ta na ɗaya daga cikin fitattun masu ƙoƙari wajen kare haƙƙin mata da yara.

Masu tattakin sun fara ne daga fadar Sarkin Katsina da ke Ƙofar Soro, inda suka ratsa tituna har zuwa Multipurpose Women Center da ke cikin birnin Katsina—inda aka ci gaba da gudanar da taro da tattaunawa kan hanyoyin rage cin zarafi, da inganta rayuwar mata, da ƙarfafa masu gwiwar wajen bayar da rahoton duk wani al’amari na take haƙƙin su.

By ukarofi