Gwamnatin Katsina za ta haɗa gwiwa da duk ƙungiyar da za ta tallafa wa harkokin ilimi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ma’aikatar ilimi a matakin farko da na sakandare Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya bayyana haka, wanda ya samu wakilcin daraktan sashen kula da makarantun ƙaramar sakandare Alhaji Kabir Dodo a wajen taron kammala gasar Turanci, da ƙungiyar bunƙasa ilimin bai ɗaya ƙarƙashin Jolly Phonics ya shirya a Katsina.

Kwamishinan ya bayyana gasar a matsayin wadda za ta ƙara ingiza ƙwazon ɗalibai, don haka ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su cigaba da tallafawa shirin, domin bunƙasa harkokin ilimin jihar.

A lokacin da shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ke jawabi, ya bayyana malamai da dama ne, suka amfana da shirin Jolly Phonics ta hanyar samun ingantaccen horo, da ya taimaka wa cigaban ilimin ɗaliban makarantun firamare a Jihar Katsina.

Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa, wadda ta samu wakilcin babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi Hajiya Ummulkairi Ahmad Bawa, ta yaba wa waɗanda suka shirya wannan shiri, tare da bayyana gasar a matsayin wadda ya nuna irin jajircewar da malaman makarantu ke nuna wa wajen koyar da ɗaliban su a Jihar.

Tun farko, jami’in shirya gasar a zhiyar Arewa maso Yammacin Nijeriya Jolly Abbas Muhammad ya bayyana cewa, shirin Jolly Phonics haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Katsina sun fara aiki tare tun a shekarar 2017, ta hanyar horaswa tare da sa ido akan yadda ake gudanar da shirin a zassan makarantun jihar.

Daga ƙarshe dai, Shiyar Funtua ce ta zo na ɗaya da maki 95 a yayin gasar ta Turanci wato (Jolly Phonics), inda shiyar Katsina ta zo na biyu da maki 89, sai kuma shiyar Daura ta zo na uku da maki 63.

By ukarofi