’Yar shara ta maida miliyan N4.8 da aka yi kuskuren sakawa a asusunta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata baiwar Allah mai shara a cibiyar kiwon lafiya, Faiza Abdulkadir ta sake nuna wa duniya cewa har yanzu akwai sauran masu gaskiya.

Fa’iza da ke karɓar albashin N30,000 a wata, ta mayar da miliyan N4.8 da aka tura cikin asusun bankinta da kuskure a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Dan uwan matar, Ibrahim Muhammad AbdulRahman ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook, ya ce duk da ƙuncin rayuwa da ta ke fama da shi, ba ta riƙe kuɗin ba.

Da take magana da manema labarai, Faiza ta bayyana cewa tsoron Allah ne ya sa ta ƙi riƙe kuɗin da ba nata ba.

Ta shaida cewa, “Kuɗin ba nawa ba ne. Na mayar da shi domin samun kwanciyar hankali, da kuma kauce wa fushin Allah a ranar lahira.”

Faiza ta ce, ta shafe kwanaki uku tana bin duk wata hanya da ta dace a bankinta kafin ta kammala mayar da kuɗin ga mai shi.

Baiwar Allah ta bayyana cewa, “Ban huta ba cikin waɗannan kwanaki uku. Har ma ban iya cin abinci da kyau ba sai ranar da na tabbatar da cewa na maida da kuɗin.”

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an banki da maƙwabta sun bayyana Faiza a matsayin mace mai gaskiya da riƙon amana, duk da cewa tana rayuwa ne a kan albashin N30,000 tare da ‘ya’yanta biyar.

“Ba mu yi mamaki ba, saboda yadda take da tarbiyya da kuma yadda take rainon ‘ya’yanta. Mace ce mai ɗabi’a da rayuwa cikin sauƙi tare da ’ya’yanta biyar.”

Wani ma’aikacin banki ya ce abin da Faiza ta yi ya burge su ƙwarai, musamman ganin halin da take ciki amma duk da haka ta zaɓi yin adalci da tsoron Allah.

Yanzu haka, labarin gaskiya da riƙon amana na Faiza Abdulkadir ya zama abin koyi ga jama’a da dama, musamman a lokacin da ƙalubale na tattalin arziƙi ke jefa mutane cikin halin wuya.

By ukarofi