Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana batun ƙarawa zaɓaɓɓu masu riƙe da muƙaman siyasa albashi musamman daga kan shugaban ƙasa, gwamnoni da ‘yan majalisu da na sauran matakai da cewa ba abin da ya kamata ba ne a cikin wannan yanayi da al’ummar ƙasar nan talakawa ke cikin mawuyacin hali.
ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ne ya bayyana hakan, yace mutane na cikin matsalolin yadda Gwamnatin Tarayya take tafiyar da su don haka hukumar da ke neman ƙara albashi ga ‘yan siyasa ta sauya shawara.
Ya ce da ana yin abin da ya dace kowa a ƙasar nan musamman ma a ce talakawa suna cikin walwala da babu wani abu, amma yanzu idan aka duba halin da ma’aikata suke ciki da albashinsu baya isarsu haka a ɓangaren jami’an tsaro ba su da albashi da zai riƙe su sannan ace za a ƙarawa ‘yan siyasa albashi ba daidai ba ne.
Ya ce idan aka yi la’akari da shugabanni masu kishi wasu ma kan saryar da albashinsu ne a hidima ta al’umma saboda ko babu albashi doka ta bada damar kyautata musu akwai haƙƙoƙi da dama da suke da ita da ake musu komai na buƙatunsu.
ɗansaran na Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ja hankalin hukumomin gwamnati da shugabanni su riƙa ƙoƙarin kawo abubuwan da talakawa za su gamsu da su kyautata cigaban rayuwarsu amma ba kawo wasu tsare -tsare na ƙarawa masu ƙarfi -ƙarfi ba alhali kuma mafi ƙarancin albashi da ake biya baya wadatar ma’aikata da su ya dace a duba.
