
Daga BELLO A. BABAJI
Nicknes Ayo wata ɗalibar makarantar sakandire ce mai shekaru 14, wadda ta kashe kanta a yankin Egba na Ƙaramar Hukumar Agatu a Jihar Benue, biyo bayan matsi da ta samu daga mahaifiyarta kan cewa ta faɗi wanda ya mata ciki.
Ayo, ɗaliba ce da ke karatu a Otukpo, wadda ta dawo gida a ranar Alhamis inda mahaifiyartan ta ga alamu na tana ɗauke da juna biyu. A nan ne ta matsa mata da tambayoyi akan ta bayyana wanda ke da alhakin hakan tare da yi mata barazanar zuwa asibiti domin yi mata gwajin juna-biyu.
Wata maƙociyarsu mai suna Mama Enyi ta ce ganin yadda mahaifiyar ta takura wa yarinyar ne ya sanya ta ficewa daga gidan, inda daga bisani aka gan ta kwance a ɗakinta sakamakon shan wani sinadari da ake kyautata zaton Gammalin’ ne.
Ta ce, nan take aka garzaya da ita wani ƙaramin asibiti domin duba halin da ta ke ciki. Ganin yadda lamarin ya tsananta, ya sa likitan ya tura su babban asibitin ƙaramar hukumar, inda akan hanyarsu ta zuwa ne aka tabbatar da rasuwarta.
Bugu da ƙari, yarinyar ta rasa mahaifinta shekaru da dama da suka gabata wanda hakan ya taimaka wajen shigarta halin matsi.
Saidai, ba a yi nasarar samun shugaban ƙaramar hukumar ko ofishin ƴan sanda ba a waya a yayin haɗa rahoton domin ƙarin bayani.
