
Daga BELLO A BABAJI
Kimanin almajirai 17 ne suka rasa rayukansu da wasu 16 da suka samu raunuka a yayin da gobara ta kama a wata makarantar Islamiyya dake ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda a Jihar Zamfara.
Gobarar ta fara ci ne daga wani gida da ke kusa da makarantar inda ta yaɗu zuwa masaukin yaran.
Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibiti don ba su kulawa.
Wani shaida mai suna Yahaya Mahi ya shaida wa manema labarai cewa da farko wutar ta kama ne a wani sashi na ginin da almajiran suke, wadda daga bisani ta bazu har zuwa ta ƙofar da za su iya tserewa, ya na mai tabbatar da mutuwar 17 daga cikinsu.
A ranar Laraba ne Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Mannir Haidara ya tabbatar da aukuwar iftila’in, inda ya ce za su bada cikakken bayani a kai daga baya.
