


Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da Ofishin Masu kula da Harkokin Sarrafa Basussuka (DMO) a ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na inganta harkoki da tsare-tsaren kuɗaɗe, wanda wani ɓangare ne na Ajendar Sabonta ƙasa ta Shugaba Bola Tinubu.
A lokacin da ya ke magana yayin zaman tawagar ofishin a Fadar Shugaban ƙasa a ranar Laraba, Shettima, wanda shi ne shugabanta, ya yi kira ga mambobi da su samar da salo na musamman wajen sarrafa kuɗaɗen bashi na al’umma.
Ya ce Nijeriya za ta cigaba da amfani da kuɗaɗen bashi a matsayin wani ginshiƙi na haɓaka tattalin arziƙin ƙasa da kuma rage matakin talauci acikin al’umma.
Shettima ya ce Nijeriya tana aro kuɗi ne bisa kulawa wanda hakan mataki ne na ciyar da tattalin arziƙinta gaba ba zama cima-zaune ba ta fuskar kuɗi.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa wajen kawo gyare-gyare ga harkar tattali, ya na mai jinjina masa wajen kawo sauyi a ɓangaren.
Ya kuma yaba wa Ministan Kuɗi da jagorancin DMO ganin yadda suke aiki tuƙuru wajen kula da lamuran basussukan ƙasa.
Har’ilayau, Shettima ya bayyana nasarar da Nijeriya ta samu a kasuwar duniya na bada Dala biliyan 2.2 daga tsarin ‘double-trenche Eurobond issuance’ a kwanan nan a matsayin abinda zai taimaka wajen janyo ra’ayoyin masu zuba hannun-jari a ƙasar.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da; Ministan Kuɗin da Shirya Tattali, Wale Edun, a matsayin mataimakin shugaba; Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, mamba; Mai taimaka wa Shugaban ƙasa akan harkokin tattali, Dakta Tope Fasua, mamba; Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, mamba; Akanta-Janar ta Ƙasa, Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein, mamba da kuma Darakta-Janar ta Ofishin kula da sarrafa basussuka, Patience Oniha, Sakatariya.
