Yarjejeniyar kare mabambanta hallitu a duniya ta Kunming da Montreal ta fidda wata hanya mai dacewa a fannin kare hallitu

DAGA CMG HAUSA

Taron COP15 ya taya murnar zartas da yarjejeniyar kare mabambanta hallitu a duniya ta Kunming da Montreal, a ranar 19 ga wata.

Matsayin wannan yarjejeniya ya yi kama da yarjejeniyar Paris, a fannin kare mabambanta hallitu, wadda ta fidda wata hanya da ta dace ga kare mabambanta hallitu nan da shekarar 2030 masu zuwa, har zuwa gaba.

Wannan yarjejeniya ta kunshi muradu 23. Daga cikinsu, abin da aka sa gaba shi ne, alkawarin kare filaye da koguna da tabkoki da tekuna da yawansu ya kai a kalla 30% a duniya kafin shekarar 2030, wanda ake kiransa “Burin 3030”.

Ban da wannan kuma, yarjejeniyar ta nuna cewa, ya kamata a samar da dalar Amurka biliyan 200 a ko wace shekara kafin shekarar 2030, don aiwatar da tsare-tsare da ayyukan tabbatar da mabambanta hallitu.

Daga cikinsu, kamata ya yi kasashe masu wadata su baiwa kasashe masu tasowa a kalla dala biliyan 20 a ko wace shekara kafin shekarar 2025, kuma a kalla dala biliyan 30 a ko wace shekara kafin shekarar 2030. Za a cika gibin karancin kudade don ba da tabbaci ga aikin kare mabambanta hallitu a duniya, idan aka iya tabbatar da wadannan alkawura.

A matsayin kasa mai rike da shugabancin taron COP15, Sin ta taka rawar a zo a gani wajen yin sulhu tsakanin bangarori daban-daban da ingiza ci gaban taron. Shugaban kasar Xi Jinping ya jaddada muhimmanci kafa kyakkyawar makomar daukar hallitu ta bai daya a cikin jawabansa, ban da wannan kuma a taro na matakin farko, an zartas da sanarwar Kunming karkashin jagorancin Sin, kazalika Sin ta kira taruka sau da dama don sauraron ra’ayin bangarori daban-daban da yin sulhu a tsakaninsu don kaiwa ga samun matsaya daya.

Mahalartan taron sun yi maraba da kokarin da Sin take yi. Wakilin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo ya yi godiya sosai ga kokarin da Sin take yi na sa kaimi ga zartas da wannan yarjejeniya.

Ana sa ran bangarori daban-daban za su ci gaba da nuna himma da gwazo a siyasance tare da daukar matakan da suka dace nan gaba kan batun kare mabambanta hallitu. (Amina Xu)