CBN ya ƙara adadin kuɗin da za a iya cirewa zuwa dubu N500

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da ƙara adadin kuɗin da mutum zai iya cirewa a banki.

Bankin ya ce, ɗaiɗaikun mutane na iya cire abin da bai wuce N500,000, sannan Naira miliyan N5 ga hukumomi a mako.

Ya ƙara da cewa, za a iya cire kuɗin ne ta duka kafofin cire kuɗin da ake da su ba tare da wani hani ba.

Wannan bayanin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da CBN ɗin ya aike wa bankuna da ita a ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne mako biyu bayan da CBN ya rage adadin kuɗin da ɗaiɗaikun jama’a za su iya cirewa a cikin banki zuwa N100,000, sannan N500,000 ga ma’aikatu.

Haka nan, Bankin ya rage adadin kuɗin da za a iya cira daga ATM da POS zuwa N20,000 a rana, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.

CBN ya ce, ya ɗauki matakin ƙara adadin kuɗin da za a iya cirewa ne biyo bayan rahotannin da ya samu daga masu ruwa da tsaki.