Hajjin 2023: Saudiyya ta maido wa Nijeriya gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ware mata

Daga BASHIR ISAH

Masarautar Saudiyya ta sake maido wa Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ba ta a baya don Hajjin 2023 idan Allah Ya kai mu.

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mousa Ubandawaki ne ya bayyana hakan ranar Laraba.

Ya ce, “Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ware Nijeriya gurbin maniyyata 95,000 da ta saba ba ta don Hajjin 2023 a ƙasa mai tsarki.

“Mai yiwuwa damar sauke farali ga ɗimbin ‘yan Nijeriya masu buƙatar hakan ta samu ke nan kasancewar Saudiyya ta maido wa NAHCON gurbin maniyyatan da ta saba ba ta kafin ɓullar Cutar Korona.

“Albishirin ya fito ne ta bakin Darakta-Janar mai kula da sha’anin Hajji da Umarah na Saudiyya, Bahauddeen Alwani, yayin ganawar da suka yi ta bidiyo tare da Shugaban NAHCON na Ƙasa, Alhaji Zukrullah Hassan,” in ji Ubandawaki.

Kazalika, ya ce Saudiyya ta janye sharaɗin adadin shekaru da na gwajin PCR yayin Hajjin 2023.

Har wa yau, ya ce Saudiyya ta bai wa NAHCON damar yin zaɓi dangane da tsarin kula da maniyyatan da ta fi buƙata daga kamfanin Mutawwiffs mai kula da harkokin Hajjin ƙasashen Afirkan da ba Larabawa ba.

A nasa ɓangaren, Shugaban NAHCON ya nuna farin ciki da godiyarsa dangane da wannan dama da Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya na ƙarin gurbin maniyyata.

Ya ce wannan abin a yaba ne maido wa ɗimbin ‘yan Nijeriya da ƙwarin gwiwa game da Aikin Hajji.

Daga nan, ya nuna godiyarsa ga Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya kan haɗin kai da goyon bayan da ta saba bai wa NAHCON wajen yi wa baƙin Allah hidima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *