A sanadin rubutu na auri matata – Abu Hisham

“Ana cin mutuncin adabi da rashin bin ƙa’idojin rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Akwai wasu mutane da Allah ya yi wa baiwa da kwarjini a rayuwar su, saboda tsarkin zuciyar su, kyakkyawan tunani da kuma ma dai wani sirrin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani. Irin waɗannan mutane ko yaya suka nemi voye kansu ba sa vata ko da a cikin dubban jama’a, sai wani abu ya fitar da hasken su. Ana samun irin su a cikin kowacce al’umma cikin su kuwa har da marubuta, fitilun al’umma. Sunan Mukhtar Musa ƙarami da ake yi wa laƙabi da Abu Hisham ba voyayye ba ne a duniyar adabin Hausa, saboda hazaƙarsa, jajircewa da sadaukarwar sa ga cigaban adabin Hausa. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja ABBA ABUBAKAR YAKUBU, marubucin ya bayyana yadda a sanadin rubutun adabi soyayya ta ƙullu tsakanin sa da wata ma’abociyar karatun littattafan Hausa, har ma kuma Allah ya ƙaddara aure a tsakanin su. Ɗan kasuwar littattafan Hausa da ya samu kansa cikin lissafin marubuta da tauraron su ke haskawa a duniyar adabi. Ga ƙarami ga Abba, a sha karatu lafiya.

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka.

ABU HISHAM: Cikakken sunana dai shi ne Mukhtar Musa Karami, amma an fi kirana da Abu Hisham. Ni ne Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Marubutan jihar Kano, kuma tsohon mai tsare-tsare na Taskar Bakandamiya, shugaban ma’aikata na ɓangaren Construction a FAB, da ke kamfanin yin takalma na Standard Footwear Nig. Limited. Ni marubuci ne kuma ina ɗan taɓa waƙa.

Ko za ka gaya mana taƙaitaccen tarihin rayuwar ka?

To, Alhamdulillahi. Ni dai haifaffen wani ƙauye ne da ake kira ɗanzaki, kilo mita goma daga cikin garin Kano, a ƙaramar Hukumar Gezawa, da ke gabas da cikin garin Kano, shekaru 35 da suka gabata. Na fara karatuna a makarantar allo, kafin daga bisani na fara karatu a makarantar firamare a ɗanzaki Primary School, bayan nan na yi Sakandire a makarantar Aliya Shahuci da ke Yakasai, har zuwa matakin Diploma a Aminu Kano College of Islamic and Legal studies. Wannan shi ne matakin neman ilimi wanda har yanzu muna kan nema. Sannan ina da aure da yara biyu, Hisham da Aisha.

Wacce gwagwarmaya ka sha a lokacin karatun ka da tasowarka, wanda ya taimaka wajen gina rayuwarka?

Tabbas na sha gwagwarmaya a lokacin karatu musamman da ya kasance tsakanin inda nake karatu da gida akwai nisa, wannan ya sa sai da na sha wuya sosai wajen zuwa inda daga ƙarshe dai aka saya min mashin mai ƙafa biyu, ina zuwa Yakasai daga ƙauyen mu na ɗanzaki daga bisani har dabara ta faɗo min nake ragewa da acaɓa duk dai don sauƙaƙa wa iyaye jigilar kuɗin mai da suke ba ni. Wannan ya sa har bayan na gama Aliya Shahuci na shiga Kwalejin Aminu Kano ba tare da wata wahala ba, musamman da ya kasance akwai mashin da zan hau in riƙa zuwa makaranta. Da haka aka samu aka kammala karatun duk da dai kafin in kammala makarantar na sayar da mashin ɗin na sayi waya (wanda yarinta ce ta kawo hakan), amma babu laifi an sha gwagwarmaya kafin samu a kammala karatun duk da muna fatan ci gaba da yin karatun a wannan lokacin.

Mai ya fara jan hankalinka kan rubuce rubucen adabi?

Dalilin da ya ja hankalina na fara rubuce-rubuce yana da alaƙa da yawan karance-karance da nake yi, wannan ya sa na ji ina so in fara gwadawa, kuma Alhamdulillahi da aka gwada ɗin sai aka dace. Yawan karatu ya yi matuƙar tasiri a kaina, dama wani malami ya ce mai yawan karatu wata rana zai zama mai rubutawa.

Wacce gudunmawa ka samu a lokacin da ka fara tunanin buga littafinka na farko?

Na samu gudunmawa ta farko ne wajen mahaifiyata, da yake kafin ƙoƙarin fara buga littafi na kasance mai sayar da littattafai ne a shagona mai suna Karami Bookshop wanda asalin samun shagon ma daga mahaifiyata ya samu. Bayan kammala rubuta littafin na samu Ayuba Muhammad ɗanzaki na ce masa ina so zan fitar da littafina kasuwa, ya yi min bayanin komai har ya kai ni gurin mai aikin Muhammad Lawan Barisa, mai kamfanin buga littafi na IYA RUWA, nan ma na samu gudunmawa sosai. Sannan sai kuma kuma daga yayana mai suna Yahaya Musa, tabbas ya yi bakin ƙoƙari wajen ba ni wasu kuɗaɗe don a samu littafin ya fita kasuwa.

Marubuta da dama na da tarihin matsalar kan-ta-waye, a tashin farko na fara fitar da littattafan su, wanne ƙalubale ka fuskanta?

Gaskiya ne wannan na fuskanci ƙalubale sosai a lokacin, duk kuwa da kasancewar Ayuba ya jagorance ni zuwa kasuwa, amma duk da haka wajen rabawa an samu matsala. Bayan an buga littafi sai aka bani su, gashi ban san kowa a kasuwa ba, duk da kuwa ina zuwa sayen littafi, amma sanin bai kai har su karbi littafina su sa a shago ba. Saboda a lokacin suna yin wani abu, ba sa fiye karɓar littafin sabon marubuci saboda a cewar su baya shiga sosai.

Da taimakon Ayuba Muhammad dai na samu na shigar da littafi kasuwa, amma wajen tattara kuɗaɗe an sha wuya, saboda a tsarinsu za ka bayar da littafi ne a kan sari, idan sun sayar da wasu a ciki sai ka je ka karɓi kudin. Da haka har su gama biyanka, a mafi yawa wanda suka yi aikin littafi su ne suke kasuwancinsa, amma mu da yake sababbi ne ƙila za su iya fuskantar rashin kasuwa, shi ya sa sai sai aka bar mu da shi. Wannan ne dai ýar matsalar da aka samu game da farkon buga littafina.

Littattafai nawa ka rubuta kuma ka fitar da su kasuwa, ba mu sunayen su da taƙaitaccen bayani game da wasu a ciki?

Na fara rubutu a 2006, ba zan manta ba ana cikin yin gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya kamar yadda ake yi a wannan shekarar 2022. Littafina na farko da na fara fitarwa kasuwa shi ne Baƙar Zuciya a 2011. Daga lokacin da na fara rubutu zuwa yanzu na ina zaton na yi littattafai sama da 26, amma guda biyu ne kawai suka fita kasuwa.

Bayan na buga littattafaina biyu BAƘAR ZUCIYA da kuma ƊOKIN SO, sai kuma na fara rubutu a online. Daga cikin littattafan da na rubuta akwai Baqar Zuciya, Ɗokin So, Mai Na Yi Wa ƙadangaru? Tsaka A Wuyanki, Tururuwa Ce Ajalina, Gafiya Ce Sanadi, sai Kunama A Daren Farko.

Sauran sun haɗa da Ban -Tafin Makauniya, Zuciyata, Baƙar Kwalba, Zanzaro, Nan Ne Gidanmu, da kuma Hayagaga.

Bakandamiya ta a litattafaina shine BAN-TAFIN MAKAUNIYA, wanda mutane suka fi so aka kuma sanni da shi na yi suna a dalilin sa shi ne ME NA Yi WA KADANGARU?

Wacce nasara ko ɗaukaka za ka iya cewa ka samu ta dalilin rubutu?

(Ajiyar Zuciya) Hmm… Nasarori. Idan aka tambayeni wacce nasara na samu na kan iya cewa a rubutu dai na fi kowa samun nasara, a tunanina. Domin kuwa a rayuwata duk wani abu da yake a gidana ban da gini mai rai da mara rai duk ta dalilin rubutu na samu. Kankat dai shi ne, na samu matar aurena ne ta dalilin rubutu kuma duk wani abu da ta zo da shi duk a ƙarƙashin dalilin rubutu ne. A kowacce irin rayuwa babu abin da ya kai ka samu mata tagari, surukai nagari, masu sanin daraja da kimar ɗan adam duk na same su ne ta dalilin rubutu.

Ga yadda abin ya fara. Littafina ya fita kasuwa a 2011. Bayan wasu watanni da fitarsa kasuwa sai na ji an kirani a waya ana yi min tambayoyi game da littafin har batun yaushe na biyunsa zai fita, abin mamaki daga garin da aka kira ni ɗin ya fi bani mamaki, an kirani ne daga Geidam ta Jihar Yobe alhalin a lokacin littafin bai fi ko wata uku da fita kasuwa ba. Wannan ya sa muka saba da wacce ta kirani, a ƙarshe Allah ya haɗa soyayyar da muka shafe shekaru biyu ana yi, ban tava ganinta ba ita ma bata tava gani na ba. A takaice dai har Allah ya kawo lokacin zuwa kuma gata yanzu haka a gidana a matsayin matar aurena. Nan ba da daɗewa ba za mu cika shekaru 8 da aure. Alhamdulillahi.

Bayan wannan akwai nasarori masu tarin yawa da na samu wanda su ma ba zan manta da su ba. Ƙungiyoyi da yawa sun karrama ni tabbas ba zan gaza wajen jero wasu daga ciki ba. Akwai Taskar Bakandamiya, Perfect Writers Association, Zamani Writers Association, Exquisite Writers Forum, Manazarta Writers Association, Duniyar Marubuta DM, da sauran waɗansu da yawa.

Sannan har wa yau akwai nasarori na jagoranci, domin kuwa na jagoranci group ɗin mu na MARUBUTA dake manhajar WhatsApp, tun daga 2017 har zuwa 2020, inda abubuwa suka yi min yawa na haƙura, a wannan lokutan mun yi abubuwa da dama masu darussa sosai ga duk wanda ya bibiya kuma ya gani. Har ta kai ga muna sanya gasa wacce muka fara a shafin MARUBUTA. Na jagoranci shirya wannan gasa da ta yi nasara tun daga 2018 da 2019 zuwa 2021. Na zama shugaban tsara-tsare na Taskar Bakandamiya, can ma mun yi abubuwa babu laifi, an sayi littattafan marubuta, an ɗauki marubuta aiki sun amfana. A 2019 na jagoranci gasar rubutu ta farko ƙarƙashin Bakandamiya, sai gasar Muhawarar Bakandamiya ta 2020. Ana cikin yin ta aka ƙara bani aikin gasar WOWEN24 2020 AWARD duk dai an kammala lafiya.

A 2021 na jagoranci gasar rubutu ta Perfect Writers Association, sai 2022 na jagoranci gasar Jarumai Writers Association, da kuma gasar Muhawarar GAMJIK wacce duk aka gudanar a wannan shekarar, sai kuma gasar Mayaƙiya da muke cikin kwamiti a yanzu. A yanzu haka ina aiki da Arewabooks da sauran wasu abubuwa da suka danganci rubutu.

Wanne abu ne ya tava faruwa da kai wanda har yanzu ba ka manta da shi ba a harkar rubutun adabi?

Abubuwa da yawa sun faru da na jin daɗi da akasin hakan. Abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba a harkar rubutu shi ne matar aure dana samu ta dalilin rubutu (na jin daɗi kenan).

Sannan ba zan taɓa mantawa da darussan da nake samu a wajen mutanen da na yi wa halacci suka nemi tozartani ba, mutane da yawa suna son shiga rayuwarka bayan sun gama shiga ka yi musu bakin ƙoƙari a ƙarshe sai su riƙa hangen ganin bayanka, duk da kuwa akwai mutanen da sai dai mu ce Allah ya jiƙan iyayensu, saboda ƙauna da suke nuna mana wacce ba za mu iya biyansu ba, sai dai mu bisu da addu’a.

Wasu babu wani amfani da muke yi musu amma kullum burinsu suka sun kyautata mana, dama kuma rayuwa gida biyu ce, mai dadi da maras dadi, kuma dole sai mutum ya rayu a guda biyun, a haka muke rayuwar rubutu da ma ta sauran wajen neman abinci, sai fatan Allah ya sa mu gama da kowa lafiya amin.

Wacce gudunmawa ka ke bayarwa ga cigaban adabi, yanzu da harkar buga littafi ta ja baya?

Babu laifi muna iya bakin ƙoƙarin ganin harkar rubutu ta ci gaba ta kowanne fanni, kamar yadda na yi bayani cewa mun buɗe zaure mai suna MARUBUTA a WhatsApp da kuma Facebook, wannan zaure ana yin abubuwa iri daban daban, mun gayyaci manyan marubuta da ƙanana don bada da kuma dabarun rubutu, an sanya gasa, don zaburar da marubuta su ƙara ƙaimi. Har zuwa yanzu jagoran MARUBUTA, Bamai A. Dabuwa, yana ta ƙoƙarin ganin komai ya ci gaba ta kowacce fuska don taimakawa marubuta.

Haka ko a Bakandamiya ita an yi abubuwa da mu babu laifi taskar Bakandamiya ta samar da abubuwa da yawa wanda muna ciki aka yi,an zo da salon sayar da littattafai don amfanin marubuta musamman da kasuwar littafi tayi ƙasa,wanda har yanzu haka ana sayen littafi a Bakandamiya.

Yanzu haka muna tare da Arewabooks inda muke ta kokarin ganin Marubuta sun kai littattafansu can don sayarwa, duk wannan cikin bayar da gudunmawa ne don ganin marubuta mun amfana. haka gasanni da muke jagoranci samar da malamai masu bayar da darussa ga marubuta. Ga kuma sabuwar ƙungiya da muka buɗe wanda a yanzu haka tana kan bakin ƙoƙarin ganin an kawo sauyi a harkar rubutu.

Wacce hanya za a bi a farfaɗo da harkar ɗab’in buga littattafai da inganta rubutun adabi?

Hanyar kawai ita ce a gyara kasuwancin littafi, don in dai kasuwar littafi ta gyaru ba sai an ce da mutum ya buga littafi ya kai kasuwa ba, saboda ya gani da ido. Inganta rubutun Adabi sai an miƙe tsaye kamar yadda muke ganin ‘yan baya suna yi, saboda yanzu zamani ya zo kowa ma marubuci ne. Sai ka duba ka ga yanda ake cin mutuncin adabi da sunan rubutu. Za ka ga an yi rubutu wanda idan irin su Farfesa Gusau suka gani tabbas za su iya fashewa da kuka saboda cin mutuncin da aka yi ƙa’idojin rubutu. Dole sai mun tsaya mu bi manya mu yi ko yi da su sannan za mu iske ci gaba a harkar.

Wanne tallafi matasan marubuta na yanzu ke buƙata daga wajen tsofaffin marubuta irin ku?

Tallafin da muke buƙata daga tsofaffin marubuta shi ne su taimaka su ja mu a jiki kamar yadda suke yi yanzu, amma mu ma matasan marubutan akwai bukatar mu yi musu biyayya. Hakan ta sa muke ta ƙoƙarin ganin mun gina wata ƙungiya da za ta kawo sauyi a wannan tsarin na tafiyar da ake yi yanzu musamman Marubutan mu na online.

Kamar yadda mafi yawa suka sani shi ne, manufofi da yawa ne suka sa aka buɗe ƙungiyar Gamjik,na farko don kawo sauyi a duniyar rubutu musamman da ake yiwa ƴan online kuɗin goro,na biyu don samar da tsari wanda zai taimaki marubuta.

Duk wayonka da dabararka idan har baka da shaida ta wata ƙungiya a rubutu to fa ci gaban da zaka samu ba zai kai yadda kake so ba,wannan yasa aka samar da wannan ƙungiya don kawo sauyi da kuma ci gaban Adabi tare da taimakon junanmu ta hanyoyi masu yawa.

Jan hankalin da zan yi mana shi ne,mu yi haƙuri da juna,dole wani zai yi maka abin da baka so wani kuma zai kawo abin da bai yi maka ba,sannan ko magana wani a rashin sani zai yi maka magana mara daɗi idan muka daure muka yi haƙuri insha Allahu za mu ga amfanin tafiyar.

Bangon littafin ‘Dokin So’

Sannan mu guji gaggawa a kowanne irin abu namu, duk abin da bai zo mana ba idan muka yi haquri a hankali za mu ga ya ƙaraso inda muke, mu sani ƙungiya da muke ciki har yanzu gininta muke yi, don haka mu yi haquri mu yi gini mai inganci ta yadda ƴan baya za su amfana ko bayan ranmu a rinƙa tuna alkhairan da muka gina.

Yaya ka ke ganin ƙoƙarin da kungiyoyi, da cibiyoyin ilimi da kafafen watsa labarai ke yi wajen shirya gasar rubutun adabi ga matasan marubuta?

Wannan yana ɗaya daga cikin tasirin da rubutu yake kara samu a idanun duniya,ci gaba ne kuma nasara ce kadan ba, a baya kafin a samu wata kafa ko wani mutum ya ɗauki nauyin gasa ana jimawa, Wasu ma idan sun fara sai ka ga sun daina, yanzu kuma ta kai ta kawo hatta ‘yan siyasa sun shiga harkar, gidan radiyo da na jaridu, mai ya janyo hakan? Tasirin rubutu kullum ƙara fitowa yake yi, kowa yana so ya ga ya amfanar da wani abu nasa ta hanyar rubutu.

Wanne abu ne ya fi ci maka tuwo a ƙwarya da ka je son ka furzar don ganin an kawo gyara a kansa game da rayuwar marubuta?

Wato a rayuwata na tsani na ga marubuta suna mayar da kansu baya, duk da kuwa wasu suna shiga a yi komai da su. Misali harkar siyasa, wanda za ka iske marubuta da yawa suna tsoron fito da ra’ayinsu, akan cewa ga wanda suke so, kuma abin da zai baka mamaki kowannensu yana da jam’iyya wanda da a ce zai yi rubutu ɗaya na cewa ga wanda yake so zai sha mamaki na ci gaban da zai samu. Rubutu yana da tasiri a gurin mutane.

Gabaɗaya wannan abubuwan da mawaƙa suke yi da marubuta za su miƙe tsaye sai sun ƙwace komai. Ba kowa ne yake jin waqa ba, amma kusan kowanne mutum yana yin facebook shi kuma ƙarfin facebook shi ne rubutu. Rubutu zai aika saqo kowacce nahiya. Mu jarraba mu shiga a yi da mu, babu wani laifi a siyasa abin kawai da ake so shi ne kiyaye mutuncinka, amma ina jin haushi sosai in ga kullum marubuta a baya da zarar an ga wani marubuci a gidan gwamanti sai ana ganin kamar ya aikata wani babban laifi.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ka?

Haƙuri Maganin Zaman Duniya.

Na gode ƙwarai da gaske.

Ni ne da godiya.