Yarjejeniyar tsagaita wuta: Hamas ta sako Isra’ilawan da ta tsare

Spread the love

Ƙungiyar Hamas mai mulkin Gaza ta sako dukkan sauran fursunonin yaƙinta da Isra’ila da ke hannunta.

Kazalika, ita ma Isra’ila ta sako wasu fursunonin Falasɗinawa da ke dankare a gidajen yarinta.

Wannan dai na cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya shata inda hakan ya sanya sojojin Isra’ila su ka tsagaita ruwan wuta kan Zirin Gaza.

Trump ya jagoranci zama inda kasar Masar, Katar da Turkiyya su ka rantaba hannu kan sulhun da a ka samar na dakatar da yakin Gaza.

Tun farko shugaba Trump ya sauka a Isra’ila ya na mai yabawa Firaminista Benjamin Netanyahu kafin ya wuce Masar inda ya halarci taron sa hannun sulhu a anguwar sararawa ta Sharma Sheikh da ke birnin Alkahira.

Kimanin shugabannin kasashe 24 su ka zauna don shaida wannan sulhun da kasashen 3 su ka sanya hannu a madadin masu tsayawa Hamas ko Falasdinawa.

Yakin Gaza da ya shafe shekaru biyu bayan kashe mutum 1200 da Hamas ta yi na Isra’ila ya haddasa mafi munin kisa na fiye da Falasdinawa 62,000 da Isra’ila ta yi a Gaza da jefa kafatanin al’ummar yankin a yunwa da rashin matsuguni.

By Babaji