An tsige Shugaban Ƙasar Madagascar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga ƙasar Madagascar sun tabbatar da cewa rundunar sojojin ƙasar ta bayyana karɓar ragamar mulkin ƙasar.

Hakan ya biyo bayan da Majalisar Dokokin ƙasar ta tsige Shugaban ƙasa, Andry Rajoelina, bisa zargin ya bar aikinsa ya gudu zuwa ƙasar waje yayin da ake zanga-zanga a cikin ƙasar.

Akan haka ne sojojin suka sanar da dakatar da kundin tsarin mulki, tare da kafa kwamitin riƙon-ƙwarya wanda ya ƙunshi jami’an tsaro, ‘yan sanda da wasu manyan hafsoshin soja.

Zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin-tashina ta samo asali ne daga tsadar rayuwa da rashin aikin yi, inda gwamnatin da ta gabata ta fara ɗaukar matakan murƙushe masu zanga-zanga.

Hakan ya janyo fushi daga sassan jama’a da kuma tallafin sojoji ga mutanen gari inda aka yi ƙoƙarin hargitsa ƙasar da nufin kawo sauyi.

By Babaji