A cikin wani mataki da ke nuna tsaurin ra’ayin gwamnatin Amurka a rikicin gabashin Jamhuriyar Demokiraɗiyyar Congo (DRC), an bayyana cewa ba za a ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da ƙasar Rwanda ba har sai dakarun Rwanda sun fice gaba ɗaya daga cikin DRC tare da dakatar da goyon bayan da ake zargin suna bai wa dakarun M23.
Wannan jawabi ya fito ne daga ofishin harkokin waje na Amurka bayan tarurrukan gaggawa da aka gudanar a Doha da kuma Washington, inda ƙasashe masu ruwa da tsaki suka nuna damuwa matuƙa kan rikicin da ya jima yana haifar da asarar rayuka da rabuwar jama’a da tasirin da rikicin ke yi ga yankin Gari ya Gabas.
Gwamnatin Rwanda, ƙarƙashin jagorancin Paul Kagame, ta ce ba za ta iya fitar da dakarunta gaba ɗaya ba saboda ‘yan tawaye masu ra’ayin FDLR na Hutu da ke cikin Congo har yanzu na barazana ne ga tsaron ƙasar. Kigali ta ce tana gudanar da matakan tsaro ne kawai domin kare kanta daga hare-haren da ke zuwa daga cikin DRC.
Sai dai Amurka ta yi watsi da wannan hujja, tana mai cewa duk wata hanyar warware rikici dole ne ta fara da janye dakarun Rwanda daga Congo, sannan a zauna a teburin sulhu cikin gaskiya da aminci.
An ƙaddamar da wani shiri mai suna Joint Security Coordination Mechanism domin duba yiwuwar kafa tsarin tsaro mai ƙarfi da riƙon amana wanda zai maye gurbin dakarun Rwanda, tare da sa idon ƙasa da ƙasa. Wannan tsarin zai haɗa da jami’an tsaro daga MDD da ƙasashen yankin kamar Angola da Kenya.
Amurka ta sanya wa tattaunawar sharadin watanni biyu kacal domin a kammala duk wasu tsare-tsare da janye dakarun kafin karshen watan Agusta 2025. Wannan ya sanya ƙasashen duniya da ƙungiyoyin rajin zaman lafiya cikin shirin ko-ta-kwana, ganin yadda wani sabon rikici ka iya sake kunno kai idan aka kasa cimma matsaya.
Majalisar ɗinkin Duniya da ƙungiyar Tarayyar Afirka sun yi kira da a dakatar da duk wata tafiya ta yaki, tare da shawarwari da za su kai ga daidaito. ƙungiyoyin farar hula daga Congo da Rwanda sun buƙaci gwamnati da shugabanni su duba halin da jama’a ke ciki maimakon sabunta yaki.
Jama’ar Kivu ta Arewa da Kudu na fuskantar hare-hare akai-akai daga ɓangarorin daban-daban. ‘Yan gudun hijira sun kai sama da miliyan biyu a yankin. Mafi yawansu na cikin sansanonin da ke fama da yunwa, rashin magani, da karancin ruwa mai tsafta.
A ƙarshe, har yanzu ba a san makomar wannan rikici ba. Amma idan Rwanda ta cika sharaɗin janye dakaru, wata kila ana iya samun hasken mafita daga duhun wannan rikici da ya daɗe yana ci wa yankin tuwo a kwarya.
